Kungiyoyin masu hada-hadar man fetur sun ce shugaba Buhari zasu zaba

Kungiyoyin masu hada-hadar man fetur sun ce shugaba Buhari zasu zaba

- Kungiyar yan kasuwar man fetur ta bayyana goyon bayan ta ga shugaba Buhari don cigaba da mulki

- Kungiyar tace mulkin shugaba Buhari ya tsaftace masana'antar

- Shugaban ya bayyana cewa kungiyar na shirin kafa matatar man fetur

Kungiyoyin masu hada-hadar man fetur sun ce shugaba Buhari zasu zaba

Kungiyoyin masu hada-hadar man fetur sun ce shugaba Buhari zasu zaba
Source: UGC

'Yan kasuwar man fetur karkashin IPMAN, a ranar juma'a ta bayyana cewa tana bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Kungiyar ta bayyana Buhari a matsayin dan takarar ta a yayin ziyarar ta ga NEC a gidan gwamnati a Abuja.

Shugaban kungiyar ta kasa Chinedu Okoronkwo da yayi magana da yawun kungiyar, ya mika godiyar su ta shugaban kasar akan tallafin shi ta masana'antar.

Yace kasar fuskantar halin kakanikayi na samar da kayayyakin man fetur kafin gwamnatin Buhari, amma yanzu abun ya canza zani.

Yace masana'antar na cike da rashawa kafin mulkin Buhari amma yanzu duk ya zama tarihi.

GA WANNAN: Onnoghen baya kunyar ma idon mutane - El-Rufai

Yace "Muna tsaye a bayan ka. A taron mu, mun yanke hukuncin goyon bayanka."

"Nasarar ka a zaben nan itace nasarar Najeriya," inji shi.

Ya kara jaddada cewa ba za a samu karancin man fetur a kasar ba har a kare zabe.

Yace kungiyar a shirye take da ta cigaba da aiki da gwamnatin Buhari don cigaba da gyara a masana'antar, yace kungiyar na shirin kafa matatar man fetur a kasar nan.

Shugaban kasa yayi godiya ga kungiyar akan goyon bayan da kungiyar ta nuna mishi.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel