Yanzu yanzu: Yan bindiga sun kai farmaki ga tawagar 'yan sanda, sun kashe ASP a Delta

Yanzu yanzu: Yan bindiga sun kai farmaki ga tawagar 'yan sanda, sun kashe ASP a Delta

- Wasu da ake kyautata zaton cewa 'yan bindiga ne sun kashe wani mataimakin Sufurtandan 'yan sanda, ASP, sakamakon harbinsa da suka yi a garin Umuachi-Afor, jihar Delta

- Jami'in dan sandan da aka kashe, ya jagoranci tawagar jami'an rundunar zuwa farautar wasu makiyaya da ke yin garkuwa da mutane a yankin

- Sai dai rundunar 'yan sandan bata bayyana sunan jami'in ba, kasancewar a cewarta har yanzu iyalansa ba su san an kashe shi ba

Wasu da ake kyautata zaton cewa 'yan bindiga ne sun kashe wani mataimakin Sufurtandan 'yan sanda, ASP, sakamakon harbinsa da suka yi a garin Umuachi-Afor, karamar hukumar Ndokwa ta Gabas, da ke jihar Delta.

Rahotanni sun bayyana cewa jami'in dan sandan, wanda kafin mutuwarsa, yana aiki a shelkwatar rundunar da ke Ashaka, kuma ya jagoranci wata tawaga ta jami'an rundunar zuwa farautar wasu makiyaya da ke kaddamar da hare hare a yankin tare da yin garkuwa da mutane, inda kuma ya gamu da ajalinsan a yayin kai sumamen.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sanda na jihar, Mr Andrew Aniamaka, a yayin tabbatar da faruwar hakan, ya ce: "Mun samu rahoton cewa anyi garkuwa da wani, inda muka tura jami'anmu domin ceto shi tare da cafke 'yan ta'addan.

KARANTA WANNAN: Nasarun minallah: Rundunar sojin sama ta tarwatsa sansanin 'yan ta'adda a Borno

Yanzu yanzu: Yan bindiga sun kai farmaki ga tawagar 'yan sanda, sun kashe ASP a Delta

Yanzu yanzu: Yan bindiga sun kai farmaki ga tawagar 'yan sanda, sun kashe ASP a Delta
Source: Depositphotos

"Akan hanyarsu, wasu da muke kyautata zaton 'yan bindiga ne suka budewa tawagar jami'an namu wuta, inda a cikin hakan ne, harsashe ya shiga jikin mataimakin Sufurtanda na rundunar wanda kuma shi ke jagorantar tawagar."

Sai dai Aniamaka, ya ki bayyana sunan jami'in rundunar da aka kashe, yana mai cewa: "Har zuwa yanzu, iyalan jami'in ba su san an kashe shi ba."

Ya ce jami'in ya mutu ne a asibitin da aka garzaya da shi bayan da 'yan ta'addan suka harbe shi.

A cewar sa: "Mun sake tura wasu jami'an namu cikin dajin domin baiwa wadanda tuni suke ciki agaji, haka zalika muna samun taimako daga tawagar tsaron sa kai ta al'ummar da ke yankin."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel