Yanzu Yanzu: An saki Shugaban APC na Abia da aka sace

Yanzu Yanzu: An saki Shugaban APC na Abia da aka sace

An saki Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) n jihar Abia, Cif Donatus Nwankpa da aka sace.

An tattaro cewa an sace Nwankpa tare da daya daga cikin hadimansa a daren ranar Litinin, 25 ga watan Janairu a hanyarsa ta zuwa Aba, cibiyar kasuwancin jihar, yan sa’o’i kadan kafin ziyarar Shugaban kasa Muhammadu Buhari zuwa jihar.

Daga bisani wadanda suka yi garkuwa dashi sun saki hadimin nasa wanda ya ji raunuka da dama.

Yanzu Yanzu: An saki Shugaban APC na Abia da aka sace

Yanzu Yanzu: An saki Shugaban APC na Abia da aka sace
Source: UGC

Masu garkuwan nashi sun sake shi ne a daren ranar Alhamis, 31 ga watan Janairu ba tare da an biya fansa ba.

Kakakin jam’iyyar ya bayyana cewa an saki jigon na APC ne bayan mambobin jam’iyyar sun roki wadanda suka yi garkuwa dashi da su sake shi ba tare da ka’ida ba, cewa shi mutumin kirki ne wanda kowa ke so.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: An yi garkuwa da shugaban jam'iyyar APC na a jihar Adamawa

A baya mun kawo maku cewa kakakin jam'iyyar APC na jihar, Kwamred Benedict Godson, ya tabbatar da faruwan haka ga yan jarida.

Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa kakakin hukumar yan sandan jihar Abiya, Geoffrey Ogbonna, ya ce an tura akalla jami'an yan sanda 1000 domin tabbatar da tsaro yayinda shugaba Buhari zai kawo ziyara jihar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel