Ba mu bari samun goyon bayan Afenifere ya dauke mana hankali ba – APC

Ba mu bari samun goyon bayan Afenifere ya dauke mana hankali ba – APC

- Jam'iyyar APC tace ba za ta bari samun goyon baya daga kowace kungiya ko yanki na kasar ya rude ta ba

- Kakakin jam'iyyar Mallam Lanre Issa-Onilu yace samun goyon baya daga wata kungiya ko yanki na kasar ba yana nufin dukkanin mutanen yankin na goyon bayan ka bane

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta yi maraba da goyon bayan da ta samu daga kungiyar Yarbawa ta Afenifere, amma ta bayyana cewa bata bari samun goyn bayan ya dauke mata hankali ba.

Da yake Magana a daren ranar Laraba, 30 ga watan Janairu, babban sakataren labarai na APC, Mallam Lanre Issa-Onilu, yace kowace kungiya na iya goyon bayan kowani dan takara amma APC ba za ta bari kowani goyon baya ya dauke mata hankaliba, jaridar New telegraph ta ruwaito.

Ba mu bari samun goyon bayan Afenifere ya dauke mana hankali ba – APC

Ba mu bari samun goyon bayan Afenifere ya dauke mana hankali ba – APC
Source: Facebook

Jam’iyyar tace samun goyon baya daga wata kungiya ko yanki na kasar ba yana nufin dukkanin mutanen yankin na goyon bayan tsayarwar bane.

A halin da ake ciki, mun samu labarin cewa Jam’iyyar All Progressive Congress (APC) a jihar Gombe tace ta kammala duk wasu tsare-tsare don zuwan Shugaban kasa Muhammadu Buhari jihar wanda aka shirya zuwan a ranar Asabar, 2 ga watan Fabrairun 2019.

KU KARANTA KUMA: Zaben 2019: Kiristoci sun yi wa Shugaba Buhari wa'azi mai ratsa zuciya

Malam Kabiru Ibn-Mohammed, babban sakataren labarai na APC a jihar ya bayyana hakan ga manema labarai a Gombe a ranar Juma’a, 1 ga watan Fabrairu.

Yace ana sanya ran Shugaban kasar wanda zai z gangamin kamfen dinsa na neman kujerar Shugaban kasa a karo na biyu zai tarbi wasu manyan yan siyasa daga jam’iyyun adawa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel