Nasarun minallah: Rundunar sojin sama ta tarwatsa sansanin 'yan ta'adda a Borno

Nasarun minallah: Rundunar sojin sama ta tarwatsa sansanin 'yan ta'adda a Borno

- Rundunar sojin sama da keatisayen LAFIYA DOLE ta kakkabe wata mabuyar 'yan ta'adda tare da kakkabe wasu daga cikin 'yan ta'addan a Arewacin jihar Borno

- Rundunar ta ce harin ya gudana ne ta amfani da jiragen yakin sama guda biyu, biyo bayan kwakkwaran rahoto da ta rundunar ta samu

- Kafin kai harin, rundunar ta tura wasu kwararrun jami'anta domin bin diddigin wasu 'yan ta'adda da suka nufi 3km da ke Arewacin garin Limberi

Rundunar sojin sama da ke hadin guiwa da rundunar atisayen LAFIYA DOLE ta kakkabe wata mabuyar 'yan ta'adda tare da kakkabe wasu daga cikin 'yan ta'addan a garin Limberi, wani karamin kauye da ke 92km a Arewa maso Yammacin garin Monguno, Arewacin jihar Borno.

Daraktan watsa labarai da hulda da jama'a na rundunar, Air Commodore Ibikunle Daramola ya yi nuni da cewa harin ya gudana ne ta amfani da jirgin yakin rundunar na sama, biyo bayan kwakkwaran bayani da rahotanni da ta rundunar ta samu da ke nuni da cewa 'yan ta'addar na samun mafaka a wani boyayyen sansani da ke garin.

KARANTA WANNAN: Kowa ya debo da zafi: APC na caccakar Atiku kan alkawarin kare barayin gwamnati

Nasarun minallah: Rundunar sojin sama ta tarwatsa sansanin 'yan ta'adda a Borno

Nasarun minallah: Rundunar sojin sama ta tarwatsa sansanin 'yan ta'adda a Borno
Source: Depositphotos

Daramola ya ce rundunar ta tabbatar da gaskiyar wannan rahoton bayan da ta tura wasu kwararrun jami'anta suka bi diddigin wasu 'yan ta'adda da suka nufi 3km da ke Arewacin muhallan jama'a, wanda kuma suka shiga mabuyar tasu.

Ya ce da wannan ne ya sa hadin guiwar rundunar sojin saman na atisayen LAFIYA DOLE ta tura jirage yaki guda biyu domin kai harin a mabuyar 'yan ta'addan a yayin da mayakan ke fitowa daga mabuyar ta su, inda aka kakkabe da yawa daga cikin su, tare da tarwatsa mabuyar wacce kuma suke amfani da ita a matsayin wajen gudanar da tarurrukansu na sirri.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta: Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel