Kowa ya debo da zafi: APC na caccakar Atiku kan alkawarin kare barayin gwamnati

Kowa ya debo da zafi: APC na caccakar Atiku kan alkawarin kare barayin gwamnati

- APC ta ce kudurin Alhaji Atiku na baiwa barayin gwamnati mafaka, tabbacine na cewa ya na son mulkar kasar ne domin wawushe kudaden da suka yi saura

- APC ta kalubalanci Atiku da abokin takararsa, Peter Obi, na kutsa kansu a cikin wani abu da suka kira "yin karya karara" da kuma "yin kazafin da ba su da hujja"

- Ta kara da cewa burin Atiku shine sayar da kadarorin da kasar ta mallaka, kana ta 'yan Nigeria da su tashi tsaye domin tabbatar da cewa Nigeria ba ta koma kamar kasar Masar ba

A ranar Alhamis, jam'iyyar APC ta ce kudurin dan takar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar na baiwa barayin kudaden gwamnatin kasar mafaka, ya bata tabbacin cewa dan takarar shugaban kasar na PDP na son dawowa shugabancin kasar ne kawai domin wawushe kudaden da suka yi saura a lalitar kasar.

Kungiyar yakin zaben dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar ta APC ta kuma kalubalanci Atiku da abokin takararsa, Peter Obi, na kutsa kansu a cikin wani abu da suka kira "yin karya karara" da kuma "yin kazafin da ba su da hujja" a lokacin da suke gudanar da taron shirin talabin mai taken "The Candidate" a daren ranar Laraba.

Jam'iyya mai mulkin ta ce dan takarar shugaban kasa karkashin PDP bai boye mummunar aniyarsa ba ta baiwa barayin gwamnatin kasar damar sake wawushe kudin kasar da kuma baiwa PDP damar sake lalata kasar, inda ta ce ya zama wajibi 'yan Nigeria su tashi tsaye domin tabbatar da cewa Nigeria ba ta koma kamar kasar Masar ba.

KARANTA WANNAN: A karon farko: Onnoghen ya yi jawabi kan makudan dalolin da ke boye a asusun bankunsa

Atiku na fuskantar kalubale kan alkwarinsa na bada kariya ga barayin gwamnati

Atiku na fuskantar kalubale kan alkwarinsa na bada kariya ga barayin gwamnati
Source: Facebook

Sakataren watsa labarai na APC na kasa, Mallam Lanre Issa-Onilu, wanda ya yi jawabi ga manema labarai a Abuja, ya ce wannan alkawarin na baiwa barayin gwamnati mafaka, ba ya daga cikin tsarin kawar da cin hanci da rashawa, amma tsari na jefa miliyoyin 'yan Nigeria cikin matsanancin halin rayuwa.

Issa-Onilu ya ce ta bayyana karara cewa takarar shugabancin kasar da Atiku ya ke yi ba wai yana yi ba ne domin ci gaban kasar, sai dai yana yi ne domin azurta abokai, 'yan uwa da kuma cimma muradun kasashen waje.

APC ta kara da cewa burin Atiku shine sayar da kadarorin da kasar ta mallaka kamar yadda ya yi a lokacin da ya ke shugabantar majalisar koli ta kasa kan sayar da kadarori da hukumomin gwamnati.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel