Anyi zanga-zangar neman tsige Onnoghen a gidan gwamnatin jihar Kaduna, hoto

Anyi zanga-zangar neman tsige Onnoghen a gidan gwamnatin jihar Kaduna, hoto

- Hadakar kungiyoyin sa kai na jihar Kaduna sunyi zanga-zangar neman a tsige CJN, Walter Onnoghen

- 'Yan kungiyoyin da suka hada da matasa da mata sun nemi a gurfanar da CJN din a gaban kuliya bayan an tsige shi

- Sun ce tunda ya amsa cewar ya sabawa doka abinda ya dace shine ya yi murabus domin tsira da sauran mutuncinsa

Anyi zanga-zangar nemen tsige Onnoghen a gida gwamnatin jihar Kaduna, hoto

Anyi zanga-zangar nemen tsige Onnoghen a gida gwamnatin jihar Kaduna, hoto
Source: Twitter

Wasu gungun masu zanga-zanga sun garzaya gidan gwamnatin jihar Kaduna inda suke bukatan a tsige alkalin alkalai na kasa, Walter Onnoghen tare da gurfanar da shi a gaban kuliya. Masu zanga-zangar karkashin hadakar kungiyoyin sai kai na jihar Kaduna sun hada da mata da matasa.

Sun ce tunda CJN na ya amsa cewar bai bayyana wasu daga cikin kadarorinsa ba kamar yadda doka ta tanadar, abinda ya dace ya aikata shine ya yi murabus daga mukaminsa domin ya tsira da sauran mutuncinsa.

DUBA WANNAN: Rarara da Ado Gwanja sun gwangwaje a wurin kamfen din Buhari

Kungiyar sun kuma yi suka ga kalaman da kasashen Amurka da Ingila su kayi a kan batun, a cewarsu kasashen na kokarin kawo cikas ne a yaki da rashawar da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari keyi.

A wani rahoton, Legit.ng ta kawo muku cewar kotun Da'ar Ma'aikata CCT ta tsayar da ranar 4 ga watan Fabrairu domin cigaba da sauraron shari'ar na Walter Onnoghen.

Dama an dakatar da Shari'ar ne bayan Onnoghen ya shigar da kara a kotun Koli inda ya nemi a hana CCT yi masa shari'a, sai dai a jiya Alhamis ne kotun tayi watsi da bukatar na Onnoghen kuam hakan ya bawa CCT damar cigaba da shari'ar.

Batun shari'ar na Onnoghen ya janyo cece-kuce tsakanin lauyoyi, al'umma har ma da kasashen ketare. Wasu na ganin dakatar da shi ne abinda ya kamata ayi yayin da wasu na ganin Shugaba Muhammadu Buhari bai bi ka'ida ba wurin dakatar da shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel