'Yan jam'iyyar PDP fiye da 3,500 sun dunguma sun koma APC a Delta

'Yan jam'iyyar PDP fiye da 3,500 sun dunguma sun koma APC a Delta

A kalla 'yan jam'iyyar People’s Democratic Party, PDP guda 3,500 ne suka sauya sheka zuwa All Progressive Congress, APC, yayin kamfen din Cif Great Ogboru da akayi daga Udu zuwa karamar hukumar Ughelli ta Kudu na jihar Delta.

Ogboru tare da Sanatan da ke wakiltan Delta ta Tsakiya a Majalisar Dattawa, Ovie Omo-Agege ya ce jam'iyyar APC ba zata razana ba da irin dabarun magudin zabe da jam'iyyar PDP ke shiryawa a jihar.

A jawabin da su kayi a filin wasanni na Otu-Jeremi da Otor-udu yayin kamfen din gwamna, sun ce, "Yan jam'iyyar APC da mutanen Delta ba za su amince da wani barazana daga PDP ba domin APC ta lashi takobin ceto mutanen Delta daga masu mulkin gado."

'Yan jam'iyyar PDP fiye da 3,500 sun dunguma sun koma APC a Delta

'Yan jam'iyyar PDP fiye da 3,500 sun dunguma sun koma APC a Delta
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Rarara da Ado Gwanja sun gwangwaje a wurin kamfen din Buhari

A cewar Ogburu, "PDP jam'iyyar duhu ce kuma a jam'iyyar APC ne kawai mutanen Delta za su ga haske da cigaba kuma ya yi kira ga wadanda suka sayar da katin zabensu su garzaya su karbo abinsu domin za a kirga kuru'u a zaben.

"Ina kira ga mutanen Delta su bawa Shugaba Muhammadu Buhari da gwamnatin APC irin goyon bayan da suke bamu domin idan ya fadi mu ma mun fadi.

"Kar ka damu da batun ceto mutane Delta domin idan kuka zabe APC kuma kuka zabe ni, Jihar Delta za ta cigaba."

A bangarensa, Sanata Agege ya ce, "Buhari ne bamu sako mu fada muku, muna magana ne a madadinsa domin ya bamu izinin wakiltarsa.

"Shugaba Buhari ya yiwa kabilar Urhobo da 'yan Delta sha tara na arziki kuma hanyar da zamu iya masa sakayya itace na jefa masa kuri'a domin ya zarce a kan mulki.

"Kusan dukkan titunan da ke jihar Delta an gina ne karkashin Hukumar NDDC karkashin gwamnatin APC da Shugaba Buhari."

A Otu-Jerem da Udu, a kalla tsaffin shugabani da 'yan jam'iyar PDP 3,500 karkashin jagorancin Cif Freeborn Ayoma da Hon. Alfred Urhukpe ne suka sauya sheka zuwa jam'iyyar APC.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel