APC ta bijire wa INEC, ta sha alwashin cike yan takara a Zamfara da Rivers

APC ta bijire wa INEC, ta sha alwashin cike yan takara a Zamfara da Rivers

- Bayan hukumar zabe ta yanke hukunci, am'iyyar APC ta yi watsi da hukuncin ta sha alwashin cike yan takara a Zamfara

- Tace ba ma a jihar Zamfara kadai ba harda jihar Rivers sai ta cike yan takara

- APC ta yi ikirarin cewa jamiyyar adawa ta Peoples Democratic Party ba ta gudanar da zaben fidda gwani ba a jihar Kano kuma INEC ba ta yi watsi da yan takararsu ba

Duk da hukuncin da hukumar zabe mai zaman kantan (INEC) ta yanke a daren ranar Laraba na hana APC gabatar da yan takara daga jihar Zamfara, jam’iyyar All Progressives Congress tace ba ma a jihar Zamfara kadai ba harda jihar Rivers sai ta cike yan takara.

Babban sakataren labarai na jam’iyyar na kasa, Mallam Lanre Issa-Onilu, ya bayyana hakan a jiya Alhamis, 31 ga watan Janairu a Abuja, jaridar Vanguard ta ruwwaito.

APC ta bijire wa INEC, ta sha alwashin cike yan takara a Zamfara da Rivers

APC ta bijire wa INEC, ta sha alwashin cike yan takara a Zamfara da Rivers
Source: Twitter

Issa-Onilu ya nace kan cewa lallai jam’iyyar ta gudanar da zaben fidda gwani a jihohin sannan cewa “za a bi duk wani hanya na doka da ya kamata don tabbatar da cewa yan takararmu sun tsaya a zaben 2019 dinnan mai zuwa a Zamfara da kuma...Rivers.”

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari yayi alkawarin sake inganta Najeriya a Kano

Yayi ikirarin cewa jamiyyar adawa ta Peoples Democratic Party ba ta gudanar da zaben fidda gwani ba a jihar Kano kuma INEC ba ta yi watsi da yan takararsu ba.

Kakakin na APC ya kara da cewa halin da ake ciki a yanzu ya nuna rashin ingancin ikirarin PDP na cewa INEC na yiwa jam’iyya mai mulki aiki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel