An raunata mutane, anyi asarar dukiyoyi yayin da 'yan APC da APM su kayi rikici a Ogun

An raunata mutane, anyi asarar dukiyoyi yayin da 'yan APC da APM su kayi rikici a Ogun

- Kazamar rikici ta barke tsakanin magoya bayan APC da APM a karamar hukumar Abeokuta ta Arewa na jihar Ogun

- Rikicin ya barke ne yayin da tawagar kamfen din jam'iyyun suka hade a wani titi da aka samu cinkosu saboda gyarar titin

- Magoya bayan jam'iyyun sun yiwa juna rauni tare da lalata dukiyoyi masu yawa kafin daga bisani 'yan sanda su shiga tsakani

Magoya bayan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da na Allied Peoples Movement (APM) sunyi kazamar fada a ranar Alhamis yayin da 'yan jam'iyyun biyu suka hade yayin gudanr da kamfen a karamar hukuma Abeokuta ta Arewa a jihar Ogun.

An raunata mutane, anyi asarar dukiyoyi yayin da 'yan APC da APM su kayi rikici a Ogun

An raunata mutane, anyi asarar dukiyoyi yayin da 'yan APC da APM su kayi rikici a Ogun
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Rarara da Ado Gwanja sun gwangwaje a wurin kamfen din Buhari

Rikicin da ya samo asali ne lokacin da tawagar dan takarar gwamnan APC, Dapo Abiodun da na dan takarar majalisar Wakilai na Abeokuta ta Arewa/Odeda/Obafemi-Owode da na dan takarar jam'iyyar APM, Mikky Kazzim suka hade a Elega Junction da ke mazaba ta 4 a karamar hukumar.

An gano cewar magoya bayan jam'iyyun sun hade ne wani wuri da ake aikin gina titi hakan ya janyo cinkoso har ta kai ga Kazzim ya sauko daga motarsa domin ya taimaka wurin rage cinkoson ababen hawan amma lokacin mutane sun harzaka kuma ganinsa ya fito sai su kayi tsamanin ya fito ya kai musu hari ne.

Sai da jami'an 'yan sanda dauke da makamai suka hallarci wurin kafin suka tarwatsa taron bayan sunyi ta harbe-harbe a iska domin razana matasan da ke fadan.

Sai dai kafin isowar 'yan sandan, magoya bayan jam'iyyar tuni sun yiwa juna illa cikin kankanin lokaci kafin daga bisani a shawo kan lamarin.

Magoya bayan jam'iyyun biyu sun jikkata kana anyi asarar dukiyoyi masu yawa kamar yadda Sahara Reporters ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel