Daraktan yakin neman zaben dan takarar gwamnan Gombe a PDP ya koma APC

Daraktan yakin neman zaben dan takarar gwamnan Gombe a PDP ya koma APC

Wani labarin da muke samu daga majiyoyin mu sun tabbatar mana da cewa daraktan yakin neman zaben dan takarar kujerar gwamnan jihar Gombe dake a shiyyar Arewa maso gabashin kasar nan a jam'iyyar PDP ya koma jam'iyyar APC.

Daraktan gangamin yakin neman zaben Dakta Bala Bello wanda aka fi sani da suna Tinka Point, ance ya bar tsohuwar jam'iyyar sa ta PDP ne sannan kuma ya koma sabuwar jam'iyyar sa ta APC ana kwanaki kadan kafin babban zaben da za'a gudanar.

Daraktan yakin neman zaben dan takarar gwamnan Gombe a PDP ya koma APC

Daraktan yakin neman zaben dan takarar gwamnan Gombe a PDP ya koma APC
Source: UGC

KU KARANTA: Dangote ya lashe wata muhimmiyar kyauta

Legit.ng Hausa dai ta samu cewa ya zuwa lokacin wallafa wannan labarin, cikakkun bayanai game sauyin shekar basu ida bayyana ba ga manema labarai a ciki da wajen jihar.

A wani labarin kuma, Dan takarar kujerar shugaban kasar Najeriya a karkashin tutar jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Atiku Abubakar ya ce karyace tsagwaron gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ke shirgawa na cewa kasar na ta saida gangar danyen mai $100 a shekara 16 da suka yi suna mulki.

Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa maganar gaskiya Shugaba Goodluck Jonathan ce kadai ta saida danyen man a wannan farashin a kuma dan wani lokacin da yayi yana mulki na shekaru biyu kacal.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel