A karon farko: Onnoghen ya yi jawabi kan makudan dalolin da ke boye a asusun bankunsa

A karon farko: Onnoghen ya yi jawabi kan makudan dalolin da ke boye a asusun bankunsa

A yayin da za a gurfanar da shi gaban kotun da'ar ma'aikata a ranar Litin, mai shari'a Walter Onnoghen, wanda aka kora daga mukamin Alkalin Alkalai na kasa, ya fayyace gaskiya kan yadda ya mallaki makudan kudaden kasashen waje da ya boye su a asusun bankunansa. Haka zalika, Onnoghen ya bayyana dalilinsa na gaza wallafa kadarorin da ya mallaka gaba dayansu.

A cikin wani jawabi da ya rubuta a sashen bincike na musamman da sa ido, na hukumar ladabtarwa CCB a Abuja, mai shari'a Walter Onnoghen, ya ce kudaden da ke a cikin asusun da ya ke ajiye kudaden kasashen waje sun fito ne daga harkar kasuwancinsa na kasashe (Forex), AGRICODE, ya yin da sauran kudaden ya same su daga saka hannun jari da ya ke yi.

A cikin jawabin, ya bayyana cewa: "Kudaden da suka shiga asusun na na Dalar Amurka, mai lamba 87000106250 bankin STD. Chartered, mai dauke da $10,000 a lokuta da dama cikin watan Yuni, 2011, sun fito ne daga kudaden da nake adanawa na tafiye tafiye na, da kuma kudaden kula da lafiyata.

KARANTA WANNAN: Yan mazabar Ondo ta kudu sun yiwa sanatansu na APC dukan kawo wuka a gaban Osinbajo

A karon farko: Onnoghen ya yi jawabi kan makudan dalolin da ke boye a asusun bankunsa

A karon farko: Onnoghen ya yi jawabi kan makudan dalolin da ke boye a asusun bankunsa
Source: Twitter

"Yana da muhimmanci in sanar da cewa kafin na bude asusun ajiye kudaden kasashen waje, ina da kudaden kasashen wajen, da na adana a gidana, saboda akwai gwamnatin da yanzu ta ke sa ido kan shige da ficen kudaden kasashen waje a hannun ma'aikatan gwamnati da suka hada da na bangaren shari'a.

"Sai dai ko a lokacin da na bude asusun, ba zan iya tuna yawan kudaden kasashen waje da na mallaka ba, saboda na yi aiki a matsayin lauya mai zaman kansa daga 1979 zuwa 1980. Wasu kudaden daga kasuwancin (forex) na AGRICODE ne, mafi yawan kudaden da nake cirewa daga asusun na biyan kudin makarantar yarana ne da ke karatu a kasashen waje da kuma saura sa hannun jari. Asusuna na kudaden Pounds da Euro a bankin STD Chartered na ajiya ne kawai."

"Danagane da zargin da ake yi mun na kin bayyana gaskiyar kadarorin da na mallaka kuwa, ni mai shari'a Walter Onnoghen, na wallafa kadarorina da na mallaka, masu lamba SCN000014 da SCN.00005 a rana daya, 14 ga watan Disamba, 2016 saboda na mance ban bayyana kadarorinba a watan Mayun 2005 bayan karewar wallafawar da na yi na shekarar 2005 da 2009."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel