Zaben 2019: Kiristoci sun yi wa Shugaba Buhari wa'azi mai ratsa zuciya

Zaben 2019: Kiristoci sun yi wa Shugaba Buhari wa'azi mai ratsa zuciya

Gamayyar kungiyar mabiya addinin kirista a Najeriya watau Christian Association Nigeria (CAN) a takaice sun yi wa Shugaba Muhammadu Buhari wa'azi mai ratsa zuciya game da zabukan gama gari da ake shirin gudanarwa da dukkan fadin kasar nan da 'yan kwanaki.

Kungiyar wadda ta yi masa wa'azain a cikin wata takardar matsaya da ta fitar bayan taron ta na lokaci-zuwa-lokaci da ta gudanar a garin Abuja, tace ya kamata ya san girman alkawari ya tabbatar da gudanar da sahihin zabe domin kaucewa rikici da zubda jini.

Zaben 2019: Kiristoci sun yi wa Shugaba Buhari wa'azi mai ratsa zuciya

Zaben 2019: Kiristoci sun yi wa Shugaba Buhari wa'azi mai ratsa zuciya
Source: UGC

KU KARANTA: Alkalin-alkalai: Wani babban masani ya fadi matsayar kan Shugaba Buhari

Haka ma kungiyar ta Christian Association Nigeria ta yi kira ga hukumomin da aiwatar da zaben ya wajaba a kan su kamar ita hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa watau INEC da kuma rundunar 'yan sanda dama sauran jami'an tsaro da su tabbatar sun kaucewa taimakon magudi.

Haka zalika kungiyar ta bayyana rashin jin dadin ta game da rashin tsaron da tace har yanzu yana matukar barazana ga yiwuwar aiwatar da zabukan cikin lumana a wasu sassan kasar nan musamman ma yankin Arewa maso gabashin ta.

Sanarwar matsayar wadda shugaban kungiyar ta Christian Association Nigeria (CAN) Rabaran Samson Ayokunle ya sanyawa hannu ya jadadda matsayar kungiyar na cigaba da baiwa gwamnatin goyon baya wajen ganin zabukan sun gudana yadda ya kamata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel