Yakin neman zabe: Babu bukatar Buhari ya je Zamfara – Sanata Kabiru Marafa

Yakin neman zabe: Babu bukatar Buhari ya je Zamfara – Sanata Kabiru Marafa

Guda daga cikin yan takarar gwamnan jahar Zamfara, Sanata Kabiru Marafa ya bayyana cewa babu bukatar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ziyarci jahar Zamfara da sunan yakin neman zabe, saboda Zamfara nasa ne, Zamfara gidansa ne.

Marafa ya bayyana haka ne cikin wata hira da ya yi da gidan rediyon BBC Hausa, inda yace sun dauke ma shugaba Buhari zuwa jahar Zamfara musamman yadda al’ummar jahar ke kaunarsa tsakaninsu da Allah.

KU KARANTA: Dalibai Musulmai sun yi barazanar mamaye jahar Legas akan bahallatsar Hijabi

Yakin neman zabe: Babu bukatar Buhari ya je Zamfara – Sanata Kabiru Marafa

Sanata Kabiru Marafa
Source: Depositphotos

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Sanatan yana cewa daga cikin dalilan da suke baiwa Buhari shawarar ya fasa zuwa jahar Zamfara shine saboda rikicin siyasar dake faruwa a jahar tsakaninsu da bangaren gwamnan jahar, Abdul Aziz Yari.

“Mun dauke ma Baba zuwa jahar Zamfara, ya bari muyi masa duk aikin da ake yi, kuma babu abinda zai taba kuri’unsa, amma idan mai girma shugaban kasa ya ga cewa yana so ya je Zamfara, toh zamu rokeshi ya sawwake mana zuwa tarbarsa a ranar da zai zo, idan har gwamnatin jahar ce za ta tarbeshi.” Inji shi

Sai dai Marafa yace bayan ta bar Zamfara, zasu shirya masa gangamin dandazon al’umma masoya, kuma suna bukatar ya aiko da wakilinsa domin ya gane ma idanunsa, sa’annan ya yi alkawarin zasu haska taron a gidan talabijin na kasa, NTA, kai tsaye.

Idan za’a tuna hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, ta jaddada matsayarta na cewa jam’iyyar APC bata da dan takara a zaben 2019 a jahar Zamfara gaba daya, wannan kuma ya biyo bayan rikice rikicen da aka sha fama da shi tsakanin bangaren Gwamna Yari da Marafa.

Wannan rikici daya samo tushe tun bayan lokacin da Gwamna Yari ya sanar da sunan kwamishinan kudi, Mukhtar Shehu a matsayin wanda yake goyon baya a takarar gwamna, ya raba kawunan jigogin jam’iyyar APC a jahar, wanda ta kai ga ba’a samu gudanar da sahihin zaben fidda gwani ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel