Yan mazabar Ondo ta kudu sun yiwa sanatansu na APC dukan kawo wuka a gaban Osinbajo

Yan mazabar Ondo ta kudu sun yiwa sanatansu na APC dukan kawo wuka a gaban Osinbajo

- Rahotanni sun bayyana cewa a ranar Alhamis, sanata mai wakiltar mazabar Ondo ta kudu, Yele Omogunwa, ya sha dukan tsiya a hannun mazauna garin Okitipupa

- Haka zalika, dan majalisar wakilan tarayya, na mazabar Idanre/Ifedore, Mr Bamidele Baderinwa, ya sha dukan kawo wuka a hannun wasu matasa a garin Idanre

- Sai dai da aka tuntubi jami'in watsa labarai na rundunar 'yan sanda na jihar, Mr Femi Joseph, ya ce babu wanda ya shigar da kara kan wannan lamari

Rahotanni sun bayyana cewa a ranar Alhamis, sanata mai wakiltar mazabar Ondo ta kudu, Yele Omogunwa, ya sha dukan tsiya a hannun mazauna garin Okitipupa, shelkwatar karamar hukumar Okitipupa, jihar Ondo, a yayin da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya kai ziyara fadar basaraken garin Idepe, Oba Michael Adetoye.

Haka zalika, a wani labarin makamancin wannan, dan majalisar wakilan tarayya, mai wakiltar mazabar Idanre/Ifedore, Mr Bamidele Baderinwa, ya sha dukan kawo wuka a hannun wasu matasa a garin Idanre, a ranar Laraba, a yayin ziyarar da Osinbajo ya kaiwa basaraken garin na Idanre.

Har sai da jami'an tsaron mataimakin shugaban kasar suka kawo dauki, tare da yin awon gaba da dan majalisar daga wajen, kana suka dai-daita jama'ar.

KARANTA WANNAN: Kar muke kallon kowa: Rabin mahalarta taron Buhari a Kano ba 'yan Nigeria ba ne - PDP

Sanata Yele Omogunwa

Sanata Yele Omogunwa
Source: Twitter

Omogunwa, wanda shine dan takarar sanatan mazabar karkashin jam'iyyar APC a zabe mai zuwa, ya kasance cikin tawagar mataimakin shugaban kasar a lokacin da lamarin ya faru.

Rahotanni sun bayyana cewa wasu matasa ne suka kai masa wannan farmakin sakamon tunzura da irin wakilcin da ya ke yi masu.

Daya daga cikin matasan wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce, "shi (sanatan) ya sha dukan tsiya ne saboda ya guje mu tun bayan da muka turashi wakilcinmu; babu wani aikin mazaba guda daya da ya taba kaddamarwa tsawon shekaru kusan hudu da muka zabe shi.

"Ba shi da wani ofishin mazaba a wannan garin; bamu da wata hanya da zamu iya zuwa mu riske shi domin sanar da shi matsalolinmu tsawon kusan shekaru hudu; don haka me ya kawo shi garinmu yanzu? Zabe na zuwa, ya zo kenan ya yaudaremu? Wannan ba zata yiyu ba."

Sai dai da aka tuntubi jami'in watsa labarai na rundunar 'yan sanda na jihar, Mr Femi Joseph, ya ce babu wanda ya shigar da kara kan wannan lamari.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta: Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel