Dalibai Musulmai sun yi barazanar mamaye jahar Legas akan bahallatsar Hijabi

Dalibai Musulmai sun yi barazanar mamaye jahar Legas akan bahallatsar Hijabi

Kungiyar dalibai Musulmai reshen jahar Legas sun yi barazanar mamaye jahar Legas gaba daya tare da hana shiga ko fita, matukar ba’a daina cin zarafin Mata Musulmai masu sanya Hijabi ba, kamar yadda shugaban kungiyar ta bayyana.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Amiran kungiyar, Malama Basheerah Majekodunmi ta bayyana haka ne a yayin wani taron manema labaru da kungiyar ta shirya a ranar Alhamis, 31 ga watan Janairu, inda tace wasu makarantu na cin zarafin dalibai masu sanya Hijabi har yanzu.

KU KARANTA: Wata Malama da ta yi fice a koyarwa ta samu kyautan kayataccen gida a Edo

Dalibai Musulmai sun yi barazanar mamaye jahar Legas akan bahallatsar Hijabi
Amira
Asali: UGC

Amira ta bayyana bacin ranta da wannan mataki ne duk kuwa da cewa gwamnatin jahar Legas ta sanar da amincewarta da duk Dalibar data ga data ta sanya Hijabi, haka zalika kotun daukaka kara ta yanke hukuncin dalibai mata Musulmai na da yancin sanya Hijabi.

“Har yanzu ana cin zarafin dalibai a makarantun gwamnati, ana fada musu bakaken maganganu, har ma ana dukansu, inda ko a makarantar sakandarin Ikosi sai da wani jami’in WAEC ya mare daliba Musulma saboda ta ki amincewa ta cire Hijabinta.

“Mun samu irin wannan matsala a makarantun sakandari dake Agbede Community Grammar School, Yewa Grammar School dake Ikorodu, da Makarantar babbar sakandari dake rukunin gidajen Iba a unguwar Ojo.” Inji ta.

Sai dai Amira tace a watan Nuwamar 2018 ne gwamnatin jahar Legas ta aika ma duk shuwagabannin makarantun sakandarin jahar umarnin su kyale duk dalibar da ta ga daman sanya Hijabi ta sa abinta akan kayan makaranta.

“Mun dauka zamu sauki bayan wannan umarni, amma abin haushi har yanzu wasu makarantu basa mutunta wannan umarni na gwamnati, don haka muke kira ga gwamnati da ta hukunta duk ire iren malaman nan, ko kuma a wayi gari wata rana mun mamaye jahar gaba dayanta tare da masu tausaya mana.” Inji ta.

Daga karshe Amira ta yi kira ga hukumar shirya jarabawar WAEC dasu sani cewa dalibai na da yancin sanya Hijabi, ba alfarma aka musu ba, don ya kamata hukumar ta ja kunnen jami’anta kan cin zarafin dalibai masu sanya Hijabi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel