Sojojin Najeriya sun karkashe yan ta’adda, sun kama kwamandansu a Borno

Sojojin Najeriya sun karkashe yan ta’adda, sun kama kwamandansu a Borno

Dakarun Sojin runduna ta 192 dake aikin tabbatar da tsaro a yankin Arewa maso gabasa sun cimma wasu gungun mayakan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram yayin da suke gudanar da aikin sintiri tare da hadin gwiwar Sojojin sa kai na Civilian JTF akan hanyar Gwoza zuwa Yamteke.

Legit.ng ta ruwaito lamarin ya faru ne a ranar Laraba, 30 ga watan Janairu, inda Sojojin suka yi kicibus da gungun yan ta’addan a lokacin da suke kokarin tsallakawa zuwa cikin jama’a, nan take suka fara bude ma Sojoji wuta, suma suka mayar musu da martani.

KU KARANTA: Yan jagaliya sun kai ma dan takarar gwamna hari yayin yakin neman zabe

Sojojin Najeriya sun karkashe yan ta’adda, sun kama kwamandansu a Borno

Rugu rugu
Source: Facebook

Sojojin basu nuna tsoro ko yin kasa a gwiwa ba, suka dinga nuna dabarun yaki dabana daban da wasa yan kwance kwance har sai da suka cimmasu inda suka kashe yan ta’adda guda hudu, yayin da sauran suka ranta ana kare dauke da raunukan harsashi da suka samu a sakamakon artabun.

Sai dai Sojojin sun samu nasarar cafke wani babban kwamandan kungiyar da bai samu nasarar tserewa ba, wanda ake yi masa inkiya da ‘Adamu rugu rugu’, dan asalin garin Gwoza, kuma shi yake jagorantar duk hare haren da Boko Haram ke kaiwa garin Gwoza.

Bayan kura ta lafa Sojojin Najeriya sun gano wasu bindigu kirar AK 47 da mayakan Boko Haram suka jefar, da wasu kananan bindigu guda biyu, da kuma alburusai da dama, kamar yadda mataimakin daraktan watsa labaru na Operation Lafiya Dole, Kanal Ado Isa ya bayyana.

Sojojin Najeriya sun karkashe yan ta’adda, sun kama kwamandansu a Borno

Yan ta'addan
Source: Facebook

Samun wannan labari keda wuya sai jama’an garin Gwoza suka dinga fitowa kan tituna suna murna, tare da jinjina ma Sojojin Najeriya da kuma bayyana godiyarsu a garesu da kama Adamu, sa’annan sun yi kira ga Sojojin dasu cigaba da kakkabe yan ta’adda a garin.

A wani labarin kuma, Dakarun rundunar Sojoji sun kai ma mayakan Boko Haram harin kwantan bauna a daidai hanyar Kumshe-Usmanari inda suka kashe dan ta’adda mutum daya, tare da jikkata wasu guda biyu da suka tsere.

Haka zalika Sojoji a jahar Borno sun kama wani dan Boko haram mai suna Mohammed Maina a unguwar Umalari dauke da kayan sawa irin na Sojoji da kuma na yansandan kwantar da tarzoma.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel