Buhari ya bayyana dalilin da yasa yake mara ma Ganduje baya duk da zargin karban daloli

Buhari ya bayyana dalilin da yasa yake mara ma Ganduje baya duk da zargin karban daloli

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi karin haske game da goyon bayan da yake baiwa gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, musamman a yayin da yake neman zarcewa akan kujerarsa, duk kuwa da zargin karbar daloli da ake masa.

Buhari ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da wani babban hadiminsa, Malam Garba Shehu ya fitar a ranar Alhamis, 31 ga watan Janairu, inda yace alakarsa da Ganduje bata shafi kokarin da yake yin a tsatface Najeriya daga matsalar rashawa ba.

KU KARANTA: Sarki Muhammadu Sunusi ya cire ma Buhari hula game wani muhimmin aiki da yake yi

Buhari ya bayyana dalilin da yasa yake mara ma Ganduje baya duk da zargin karban daloli

Buhari Ganguje
Source: Facebook

Legit.ng ta ruwaito shugaba Muhammadu Buhari yace akwai banbanci tsakanin zargi da kuma gaskiya, don haka yace a yakin da yake yi da rashawa babu zancen shafaffu da mai ko akasin haka.

Bugu da kari fadar shugaban kasa tayi misali da wasu manyan jami’an gwamnatin Buhari wanda a yanzu haka suke fuskantar tuhume tuhumen da suka danganci cin hanci da rashawa a gaban kotuna daban daban, ciki har da tsohon sakataren gwamnati Babachir.

Sauran sun hada da babban sakataren hukumar inshoran lafiya, Usman Yusuf wanda a yanzu haka aka sallameshi daga aiki har sai an kammala bincike akan tuhume tuhumen rashawa dake wuyansa, da kuma tsohon gwamnan Filato Joshuwa Dariye da a yanzu haka yake zaman gidan kaso.

Don haka sanarwar ta cigaba da cewa daga cikin wadanda ake tuhuma akwai wadanda suke kusa da shugaban kasa, amma hakan bai hana a bincikesu ko gurfanar dasu gaban kotu ba, don haka babu wani shafaffe da mai a yakin da yake yi da rashawa.

Dangane da Ganduje kuwa, sanarwar ta bayyana cewa a matsayinsa na gwamna yana da kariya da dokar kasa ta bashi, musamman game da abinsa ya shafi gurfana gaban kotu ko shigar da kararsa, sa’annan dokokinmu sun hana kama mutum da laifi har sai kotu tabbatar da laifin akansa.

“A halin yanzu, maganan Ganduje na gaban kotu, kuma shugaban kasa bashi da ikon juya kotu ko majalisar dokokin jahar Kano wanda take gudanar da bincike akan lamarin.” Inji Garba Shehu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel