Onnoghen baya kunyar ma idon mutane - El-Rufai

Onnoghen baya kunyar ma idon mutane - El-Rufai

- Onnogen ya tafka rashin da'a inji El-rufai

- Yace bai cancanta ya cigaba da rike mukamin alkalin alkalan Nigeria ba

- Ya bukaci yan Nigeria su cigaba da goyon bayan shugaba Buhari wajen yaki da cin hanci da rashawa

Onnoghen baya kunyar ma idon mutane - El-Rufai

Onnoghen baya kunyar ma idon mutane - El-Rufai
Source: Depositphotos

Gwamnan jihar Kaduna Nasir Ahmad El-l-rufai yace tsohon alkalin alkalin Nigeria Onnogen ya aikata abun kunyar da bai cancanta ya cigaba da zama a mukamin sa ba.

Kuma ya kara da cewa matakin da shugaba Buhari ya yanke na dakatar dashi yayi daidai saboda ko kadan bai cancanta ya cigaba da rike mukamin alkalin alkalai ba.

Elrufai ya fadi hakane a lokacin da yake jawabi ga dubunnan mutanen da suke fito zanga zanga don ganin an sauke alkalin alkalan.

GA WANNAN: Sabbin kusoshi da Obasanjo ya aikowa Buhari a yau

An dai dakatar da Onnogen ne sakamakon zarge zargen badakalar cin hanci da rashawa da ake ganin tsohon alkalin ya samu kansa dumu dumu a ciki.

Hakan ya kawo kace nace akan lamarin inda kungiyar lauyoyi ta kasa take ganin matakin da Buhari suke ganin ba a yiwa tsohon alkalin adalci ba har suke bukaci lauyoyi su kauracewa kotuna domin nuna rashin jin dadin su ga hukuncin shugaban kasar.

An dai sauke Onnoghen ne bayan mantuwa da yayi bai fadi kudaden sa da ya boye a kasashen waje ba, miliyoyin daloli.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel