Ai ko don kunyar iyali na na karasa gadar gabashin Najeriya ta 2nd Niger Bridge - Atiku

Ai ko don kunyar iyali na na karasa gadar gabashin Najeriya ta 2nd Niger Bridge - Atiku

- Atiku yayi alkawatin karasa gadar Niger ta biyu matukar aka zabe shi

- Tsohon mataimakin shugaban kasar yace zai yi haka ne saboda matarshi yar asalin birnin kasuwancin jihar Anambra ce

- Dan takarar yaje har fadar Obi na Onitsha don bukatar basaraken yasa mishi albarka

Ai ko don kunyar iyali na na karasa gadar gabashin Najeriya ta 2nd Niger Bridge - Atiku

Ai ko don kunyar iyali na na karasa gadar gabashin Najeriya ta 2nd Niger Bridge - Atiku
Source: Depositphotos

Dan takarar shugabancin kasa karkashin jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar yayi alkawarin karasa gadar Niger ta biyu matukar aka zabe shi.

Atiku, wanda yayi alkawarin a jiya yayi babban zagayen kamfen din shi a Onitsha, yace zai tabbatar da an gaggauta kammala gadar saboda matarshi daga birnin kasuwancin jihar Anambra take.

Ai ko don kunyar iyali na na karasa gadar gabashin Najeriya ta 2nd Niger Bridge - Atiku

Ai ko don kunyar iyali na na karasa gadar gabashin Najeriya ta 2nd Niger Bridge - Atiku
Source: UGC

Yayi alkawarin tabbatar da kammaluwar tare da gyara tituna a yankin da taimakon mataimakin shi, Mr Peter Obi.

Atiku,wanda ya samu rakiyar Obi da matar shi Jennifer Atiku Abubakar, yace bai je Onitsha don yakin neman zabe kadai ba harda gabatar da matarshi da mataimakin shi, wadanda yace sune asalin masu takarar.

"Banzo kamfen ba amma nazo ne don sanar daku cewa danku, Peter Obi da yar ku sune asalin yan takarar. Ni karami ne. Kun umarce ni da in kammala gadar Niger ta biyu wanda zanyi saboda matata. Da peter Obi a matsayin mataimaki na, ku tabbatar cewa titunan yankin nan zasu kammala," inji Dan takarar.

Ya shawarci mutanen dasu mallaki katin zaben su na dindindin don tintsirar da gwamnatin shugaban kasa Buhari a zaben watan Fabrairu mai zuwa. Ya kuma shawarce su dasu zabi PDP.

Shugaban jam'iyyar PDP, Prince Uche Secondus, wanda ya gabatar da yan takarar, ya roki mutane dasu zabe su.

A lokacin da ya kaiwa Obi na Onitsha ziyara, Obi Alfred Achebe, Atiku ya bukaci albarkar basaraken, wanda kamar yanda yace zata bunkasa burin shi na bunkasa tattalin arzikin kasar nan.

GA WANNAN: Daga Buharin har Atiku bana yi' inji Wole Soyinka

"Albarkarka ta sarauta zata raini burin mu na sabuwar alkiblar tattalin arzikin kasar nan ta hanyar samar da sabuwar siyasa."

Ya kuma tabbatarwa da basaraken cewa sababin dokoki da zai bullo dasu zasu bunkasa al'adu da bude ido na kasar nan.

A jiyan Atiku yayi alkawarin farfado da tashoshin jiragen ruwa dake jihar Delta matukar aka zabe shi.

Atiku da yayi jawabi game wadanda sukayi imani da PDP ya samu rakiyar mataimakin shi, shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki, Secondus da gwamnan jihar Delta, Gwamna Ifeanyiy Okowa.

Yace mulkin shi zai tabbatar da ya kammala aiyukan da gwamnatin tarayya karkashin APC ta watsar, kari da cewa gwamnatin ta bar aiyukan ne ganin cewa jihar na biyayya ne ga PDP.

Atiku yace gada ta biyu ta Niger zata samu fifiko daga gwamnatin shi.

Yace gwamnatin shi zata sakawa biyayyar da jihar Delta kewa PDP tun 1999.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel