Gwamnati ta kwace wata marainiyar N1.05b wadda uwarta ta gudu ta barta

Gwamnati ta kwace wata marainiyar N1.05b wadda uwarta ta gudu ta barta

- An bawa hukumar yaki da rashawa ajiyar kudi har 1,000,494,000 na wucin gadi

- An samu kudin ne a bankin Fidelity, a asusun kamfani mallakin Patience Jonathan

- An gano cewa kamfanin mallakin ta ne da wasu yan uwan tsohon shugaban kasar

Gwamnati ta kwace wata marainiyar N1.05b wadda uwarta ta gudu ta barta

Gwamnati ta kwace wata marainiyar N1.05b wadda uwarta ta gudu ta barta
Source: UGC

An bawa hukumar yaki da rashawa ajiyar kudin da aka kwace har Naira biliyan 1,000,494,000 na wucin gadi.

An kwace kudin ne sakamakon karar da hukumar ta kai na a kwace su daga boyayyen asusun bankin MAGEL RESORT LIMITED, kamfanin da yake da hadi da matar tsohon shugaban kasar Najeriya, Patience Jonathan.

Hukumar ta samu rahoton sirri cewa wani asusun banki a bankin Fidelity yana shakare da kudi wadanda babu wanda ke amfani dasu.

Bayan samun bayanin sirrin ne hukumar ta fara bincike wanda ya bayyana cewa uwargidan tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan da wasu yan uwan Goodluck ne mamallakan kamfanin.

GA WANNAN: Kungiyar Ohanaeze ta Ndi-Igbo, ta dakatar da sakatarenta kan 'azarbabinsa'

Sauran mamallakan kamfanin sun hada da Oba Oba Tamunotonye, Goodluck Jonathan Aruera, Goodluck Jonathan Ariwabai da Esther Fynface.

Yayin gano asalin kudin, hukumar ta gano cewa a ranar 20 ga watan Mayu 2015, Esther Fynface ta zubawa asusun bankin Naira dubu dari biyar, wacce ake zargin itace ke rike da kamfanin. An gano cewa an tura Naira biliyan daya daga PAGMAT OIL AND GAS LIMITED a 25 ga watan Mayu.

Kotu tace ta bada damar kwace kudin na wucin gadi inda za a zuba su a asusun tarayya.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel