Magun EFCC ya gargadi bankuna kan kudaden taimakawa ta'addanci dake yawo

Magun EFCC ya gargadi bankuna kan kudaden taimakawa ta'addanci dake yawo

- Bankuna kan boye wa 'yan siyasa kudi

- Wasu kudaden ana laifuka dasu

- EFCC ta sanya ido kan yadda kudaden ke zagaye

Magun EFCC ya gargadi bankuna kan kudaden taimakawa ta'addanci dake yawo

Magun EFCC ya gargadi bankuna kan kudaden taimakawa ta'addanci dake yawo
Source: Facebook

Ibrahim Magu, dansanda dake kula da ayyukan tu'annati kan tattalin arziki watau EFCC, ya aike kashedi ga manyan bankunan kasar nan dake kokarin boye kudaden jama'a da ake taya tsofi da sabbin barayi, kudade da ake laifuka dasu.

A cewarsa, bankuna su kuka da kansu su bar taimakawa masu kudin boye, inda wasu daga kudaden, ba na halak malak bane, kuma ana iya amani dasu wajen taimakawa ta'addanci da ma aikata miyagun laifuka da 'tsakar dare'.

GA WANNAN: Chabb! Shekararta 14 kacal amma ta iya satar N3.5m, an sanya ta kurkuku

A jiya alhamin yake wannan jawabi, a taron Association of Chief Compliance Officers of Banks In Nigeria (ACCOBIN) da aka yi a Lagos, wanda ke duba hanyoyi da za'a daqile muguwar aqidar nan ta adana kudade.

Magu, yace ya kula da yawa daga manyan barayin Najeriya, sun fara dawo da kudaden da suka sata suka boye a baya, a kasashen waje, inda yace yanzu kau sun fara dawo da wadannan kudade cikin najeriya domin kamfe son su ci zabe.

Ya kuma ce wasu 'yan siyasar na amfani da wadannan kudade, domin ko sayen kuri'u, ko tada zaune tsaye, ko ma tayar da hankalin jama'a domin cimma burikansu na siyasa.

Mr Wumi Adeniyi, mataimakin shugaba a ACCOBIN din, yace suna godiya da karrama su da amsa gayyatar da suka yi ma shugaban na EFCC.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel