Mai Shari’a ya hana Shekarau zuwa tarbar Buhari a Kano

Mai Shari’a ya hana Shekarau zuwa tarbar Buhari a Kano

Alkalin babbar kotun tarayya, Lewis Alagana, ya hana tsohon gwamnan jihar Kano, Mallam Ibrahim Shekarau zuwa tarbar Shugaba Muhammadu Buhari wanda ya kaddamar da kamfen dinsa a jihar Kano a yau Alhamis, 31 ga watan Janairu.

Hakan na daga cikin rangajin da Shugaban kasar ke yi na neman tabbaraki daga al’umman kasar domin ya samu ya zarce a zaben ranar 16 ga watan Fabrairu da za a gudanar.

Ana tuhumar Shekarau da hannu wajen karbar naira miliyan 950 daga tsohuwar ministar fetur, Diezani Alison-Maduekwe wanda kudi ne da aka rarraba domin kamfen din zaben 2015 a karkashin gwamnatin tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan.

Zaman kotun ke da wuya a yau Alhamis, sai lauyan Shekarau mai suna Jibrin Okutepa, ya mike ya nemi alkali ya dage karar domin Shekarau ya samu damar zuwa tarbar Buhari.

Alkali Alagana ya ki amincewa, ya nuna cewa wannan ba wani kwakwaran dalili da zai sa ya dage sauraren karar ba ne.

Mai Shari’a ya hana Shekarau zuwa tarbar Buhari a Kano

Mai Shari’a ya hana Shekarau zuwa tarbar Buhari a Kano
Source: Depositphotos

Bayan an jima, lauya Okutepa ya sake mikewa a karo na biyu, ya nemi a dage shari’ar. Ya na mai cewa:

“Ya Mai Girma Mai Shari’a, wanda na ke karewa dan siyasa ne, kuma ya na cikin wadanda Buhari zai mika wa tutar takarar sanata a yau wurin taro. Ina so a dage sauraren shari’ar nan, domin ya samu halarta."

Alkali ya ki amincewa, inda ya ce za a ci gaba da shari’ar a haka.

Nan take sai mai gabatar da kara daga Hukumar EFCC, wato Samuel Chinwe, ya gabatar da shaida na farko, wanda ya shaida wa kotu cewa ya samu rahoton sirri da ya tabbatar da cewa an narka wasu makudan kudade har naira biliyan 23 a wani asusu a Fidelity Bank, Legas.

KU KARANTA KUMA: Zargin cin hanci: Gwamna Ganduje ba zai kamu ba yanzu - Inji Buhari

Ya ce kudin daga Diezani, ministar fetur ta lokacin suka fito. Mai gabatar da shaida ya ce an kamfaci naira milyan 950 an bai wa Aminu Wali da Masur Muktar, jiga-jigan PDP na Kano a lokacin.

Ya ce an ba su kudaden a ranar 23 Ga Maris, 2015, ana saura kwana biyu zabe.

Mai Shari’a ya ce za a ci gaba da shari’ar a gobe Juma’a, 1 ga Fabrairu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel