Dalilin hana a kara wa tsohon shugaban EFCC girma zuwa DIG

Dalilin hana a kara wa tsohon shugaban EFCC girma zuwa DIG

- An bankado dalilin cire sunan tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da hana yiwa tattalin arziki zakon kasa daga cikin sunayen manyan ‘yan sandan da aka kara wa girma zuwa DIG

- Bincike ya nuna akwai wasu manyan jami’an har guda hudu da ke gaba da shi a wajen mukami da dadewa

- Ana ganin dalilin haka ne aka cire sunan sa

Rahotanni sun kawo cewa an bankado cewa an cire sunan tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da hana yiwa tattalin arziki zakon kasa (EFCC) daga cikin sunayen manyan ‘yan sandan da aka kara wa girma zuwa DIG saboda wasu dalilai.

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa an ki kara masa girma ne saboda akwai wasu manyan jami’an har guda hudu da ke gaba da shi a wajen mukami da dadewa. Ana ganin idan aka kara masa girma zuwa DIG su kuma ba a kara musu ba, to abin zai janyo cece-kuce da rabuwar kai.

An tattaro cewa Lamorde shi ne babba daga cikin kwamishinonin ‘yan sanda 95 na kasar nan, ya na cikin wadanda aka rattaba cewa za a kara musu girma zuwa Babban Mataimakin Sufeto Janar.

Dalilin hana a kara wa tsohon shugaban EFCC girma zuwa DIG

Dalilin hana a kara wa tsohon shugaban EFCC girma zuwa DIG
Source: UGC

Sai dai kuma yayin da aka fito da sunayen wadanda aka yi wa karin, sai ba a ga sunan Lamorde a ciki ba.

Majiya ba daya ba a cikin ‘yan sanda ta sanar da cewa akwai Mataimakan Sufeto Janar har hudu daga yankin Arewa maso Gabas inda Lamorde ya fito, wadanda sun fi shi mukami.

KU KARANTA KUMA: Zargin cin hanci: Gwamna Ganduje ba zai kamu ba yanzu - Inji Buhari

Ana ganin dalilin haka ne aka cire sunan sa, shi ya sa ba a kara masa girma yadda zai wuce su ba.

Amma wata majiya ta ce nan gaba za kara masa girma zuwa Mataimakin Sufeto Janar, wato AIG, maimakon Babban Mataimakin Sufeto Janar, wato DIG da aka nemi a cilla shi kwanan nan, kafin a canja tunani a cire sunan sa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel