Zargin cin hanci: Gwamna Ganduje ba zai kamu ba yanzu - Inji Buhari

Zargin cin hanci: Gwamna Ganduje ba zai kamu ba yanzu - Inji Buhari

Fadar Shugaban kasa ta bayyana cewa Gwamna Abdulallahi Ganduje na jihar Kano ba zai iya fuskantar hukunci akan zargin karbar cin hanci ba saboda a yanzu yana da kariya daga duk wani hukunci a matsayinsa na gwamna mai ci.

Garba Shehu, babban mai ba Shugaban kasa shawara na musamman a kafofin watsa labarai ya bayyana hakan a ranar Alhamis, 31 ga watan Janairu, lokacin da yake watsi da ikirarin cewa cudanya da Shugaban kasar ke yi da Gwamna Abdullahi Ganduje ya saba ma yaki da rashawa.

Hadimin Shugaban kasar ya bayyana cewa Ganduje na da kariya a kundin tsarin mulkin Najeriya saboda haka kuma wansa ake zargi ba mai laifi bane har sai kotu ta tabbatar da laifinsa.

Zargin cin hanci: Gwamna Ganduje ba zai kamu ba yanzu - Inji Buhari

Zargin cin hanci: Gwamna Ganduje ba zai kamu ba yanzu - Inji Buhari
Source: UGC

Shehu ya ci gaba da cewa lamarin Ganduje na a kotu sannan cewa Shugaban kasar bai da ikon yiwa kotu ko majalisar dokokin jihar Kano katsalandan, wanda tuni suka fara bincike akan lamarin, da kuma abunda za a yi kan zargin da ake yiwa Gandujen.

KU KARANTA KUMA: 2019: APC ta yi babban rashi a Akwa Ibom yayinda manyan jam’iyyar da magoya bayansu suka koma PDP

Ya kuma yi watsi da ikirarin cewa Shugaban kasar na kare wadanda ked a kusanci da shi, cewa babu wani jami’in gwamnati da zai tafi ba tare da hukunci ba idan har aka kama shi da laifi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel