Gobara tayi mummunar barna a jihar Kano

Gobara tayi mummunar barna a jihar Kano

Hukumar 'yan kwana-kwana dake kashe gobara ta jihar Kano a shiyyar Arewacin Najeriya tace wata gobara ta lashe shagunan 'yan kasuwa na wucin gadi har hudu a kasuwar Mariri da ake saida itace a karamar hukumar Dawakin kudu ta jihar.

Jami'in hulda da jama'a na hukumar Alhaji Saidu Mohammed shiya ya sanarwa da manema labarai hakan a ofishin sa dake a hedikwatar hukumar a jihar ta Kano.

Gobara tayi mummunar barna a jihar Kano

Gobara tayi mummunar barna a jihar Kano
Source: UGC

KU KARANTA: Atiku ya kaso jirgin karyar Buhari da Obasanjo

Legit.ng Hausa ta samu cewa Alhaji Saidu ya ce da tsakar daren ranar Alhamis ne suka samu kiran al'ummar yankin ta hannun wani Isma'il Mohammed wanda ya shaida masu halin da ake ciki.

Alhaji Sa'idu ya kara da cewa hakan ke da wuya sai ma'aikatan su suka garzaya suka nufi unguwar cikin motocin su dauke da ruwan kashe gobara da sauran kayayyakin aiki.

Ya cigaba da cewa da zuwan jami'an nasu ne sai suka shiga aiki inda suka samu nasarar murkushe gobarar suka kuma hanata bazama ya zuwa wasu shagunan dake kasuwar.

Ya zuwa yanzu dai hukumar ta ce tana kan bincike kan dalilin gobarar.

A wani labarin kuma, Dan takarar kujerar shugaban kasar Najeriya a karkashin tutar jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Atiku Abubakar ya ce karyace tsagwaron gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ke shirgawa na cewa kasar na ta saida gangar danyen mai $100 a shekara 16 da suka yi suna mulki.

Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa maganar gaskiya Shugaba Goodluck Jonathan ce kadai ta saida danyen man a wannan farashin a kuma dan wani lokacin da yayi yana mulki na shekaru biyu kacal.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel