INEC ta fitar da sunayen ‘yan takarar 2019 babu sunan ‘Yan APC a Ribas

INEC ta fitar da sunayen ‘yan takarar 2019 babu sunan ‘Yan APC a Ribas

- INEC ba ta ba Jam’iyyar APC a Ribas damar shiga cikin zaben 2019 ba

- Babu ‘Dan takarar APC da zai nemi kujerar Gwamna ko Majalisa a Ribas

- Hukumar zaben ta bi umarnin Kotu ta haramtawa APC shiga zaben 2019

INEC ta fitar da sunayen ‘yan takarar 2019 babu sunan ‘Yan APC a Ribas

Babu ‘Yan takarar APC a cikin wadanda za su yi zabe a Ribas
Source: Depositphotos

Mun ji labari dazu cewa jerin karshe na sunayen ‘yan takarar da za a fafata da su a zaben 2019 ya fito inda aka ga cewa har yanzu hukumar zabe na kasa ba ta saka ‘yan takarar jam’iyyar APC a cikin wadanda za su yi zaben ba.

A makon nan ne hukumar INEC mai zaman kan-ta, ta kammala fitar da sunan wadanda za su tsaya takara a zaben 2019. A cikin jerin da aka fitar na masu neman mukamin gwamnan jihar da kuma ‘yan majalisa babu ‘yan takarar APC.

KU KARANTA: APC tayi wa wani babban kusa a Jam’iyyar PDP wankan tsarki

Kwanaki wani babban Alkali ya soke zabukan da jam’iyyar APC tayi wajen fitar da ‘yan takarar ta, wannan ya sa hukumar zabe mai zaman kan-ta watau INEC ta cire ‘yan jam’iyyar APC daga cikin wadanda za ayi zaben 2019 da su.

A jeringiyar ‘yan takarar da aka fitar kwanan nan, an ga sunayen masu neman takara a karkashin jam’iyyar PDP, har ma da sauran jam’iyyun hamayya irin su SDP, Labour Party, amma babu ‘yan takarar APC gaba daya a cikin jerin.

Channels TV ta dauki hoton sunayen da INEC ta lika a makon nan, inda aka duba tun daga sama har kasa babu ko ‘dan takarar guda daga cikin mai neman mukami a jihar Ribas daga cikin bangaren APC na Tony Cole da Magnus Abe.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel