An damke wata Mata da ke kokarin sace wani ‘Dan makaranta a Ghana

An damke wata Mata da ke kokarin sace wani ‘Dan makaranta a Ghana

- An kama wata Baiwar Allah tana kokarin sace yaro daga makaranta

- Har bidiyon yadda Mahaifin wannan yaro ne yayi ram da wannan mata

- Mutane sun cafke matar a daidai lokacin da ta ke yin wannan ta’adi

An damke wata Mata da ke kokarin sace wani ‘Dan makaranta a Ghana

Masu satar mutane sun shiga hannun Jama’a a Ghana
Source: Facebook

Dazu labari ya zo mana na wata mata da ta shiga hannun jama’a a lokacin da ta ke yunkurin dauke wani yaro a makarantar boko. Wannan mata tana cikin irin masu sace yaran mutane su na garkuwa da su ko kuma wani mugun nufi na dabam.

Wannan abu ya faru ne a kasar Ghana mai makwabtaka da Najeriya inda wannan ta shigo har makaranta tana neman sace wannan karamin yaro. Wannan mata dai tayi shiga ne kamar ita ce Mahafiyar yaron da nufin yin gaba da shi.

KU KARANTA: Ana neman a taimakawa Buhari wajen maganin Barayin Najeriya

Kamar yadda mu ka samu rahoto daga shafin Ghanapage.com inda aka nuna har bidiyon yadda wannan mata ta nemi sace yaran mutane ana zaune kalau. Ba ta kai ga wannan shiri ba dai jami’an tsaro su cafke ta aka jefa a cikin mota.

Babu mamaki za a mika ta a gaban hukuma ne inda za a yanke mata hukunci. A bidiyon an ga wannan mata tana rufe fuskar ta bayan ta shiga hannun jama’a. A kasashen Ghana da ma Najeriya, satar jama’a yana nema ya zama ruwan dare.

Idan ba ku manta ba, kwanan nan ne aka sace wani shugaban jam'iyyar APC mai mulki a Kudancin Najeriya a daidai lokacin da aka ji labarin cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari zai shiga garin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel