Yan jagaliya sun kai ma dan takarar gwamna hari yayin yakin neman zabe

Yan jagaliya sun kai ma dan takarar gwamna hari yayin yakin neman zabe

Yan jagaliya sun kai ma ayarin motocin dan takarar gwamnan jahar Legas a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, Jimi Agbaje hari a ranar Alhamis, 31 ga watan Janairu, a unguwar Iba, cikin karamar hukumar Ojo West, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito matasan sun kai ma dantakara Jimi hari ne a daidai lokacin da ya fito daga fadar sarkin Iba, Oba Gorolia Oseni, inda suka shiga jifansa a manyan duwatsu da sauran abubuwan jifa.

KU KARANTA: An kaure da cacar baki tsakanin Ummi Zee Zee da Zaharaddeen Sani tare da nuna ma juna yatsa

Gwamnan ya tafi fadar Sarkin ne da nufin ya bayyana masa manufarsa ta tsayawa takarar gwamnan jahar Legas a ranar Alhamis, amma fitowarsa keda wuya sai ya ci karo da fusatattun matasan, da adadinsu ya kai 40 dauke da muggan makamai.

Ganinsa keda wuya suka ce da wa Allah ya hadamu idan ba kai ba, nan take suka shiga jifansa, wanda a sakamakon haka suka farfasa gilasan motocin dake cikin ayarinsu, haka suka cigaba da jifansa har sai ya tsere.

Haka zalika wasu daga cikin jiga jigan yayan jam’iyyar PDP da suka take ma Jimi baya sun samu rauni daban daban a sakamakon harin, bugu da kari matasan sun raka ayarin motcin da nufin far musu, amma aka ci sa’a jami’an Yansanda suka shiga tsaninsu.

Yansanda sun yi kokari suka fatattaki yan jagaliyan, amma basu samu nasarar cafke kowa daga cikinsu ba, sai dai rahotanni sun tabbatar da cewar dan takarar gwamnan PDP bai samu wani rauni ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel