2019: APC ta yi babban rashi a Akwa Ibom yayinda manyan jam’iyyar da magoya bayansu suka koma PDP

2019: APC ta yi babban rashi a Akwa Ibom yayinda manyan jam’iyyar da magoya bayansu suka koma PDP

- Jam’iyyar APC ta rasa wasu mambobinta a jihar Akwa Ibom

- Tsohon shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa, Sanata Godeswill Akpabio ne shugaban APC a jihar

- Tsohon dan majalisar wakilai Bassey Dan-Abia na cikin wadanda suka sauya shekar

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Akwa Ibom ta sake babban rashi sakamakon sauya sheka da manyan jiga-jigan jam’iyyar a karamar hukumar Esit Eket, Bassey Dan-Abia da Emem Edoho suka yi zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) tare da tarin magoya bayansu.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Dan Abia jnr, wani tsohon dan majalisar wakilai na mazabar Eket, ya kasance kani ga tsohon manajan darakta na hukumar ci gaban Niger Delta, Bassey Dan Abia.

2019: APC ta yi babban rashi a Akwa Ibom yayinda manyan jam’iyyar da magoya bayansu suka koma PDP

2019: APC ta yi babban rashi a Akwa Ibom yayinda manyan jam’iyyar da magoya bayansu suka koma PDP
Source: Twitter

Legit.ng ta tattaro cewa masu sauya shekar sun bar tsohuwar jam’iyyarsu ta APC, tare da daruruwan magoya bayansu lokacin da PDP ta kai kamfen dinta yankin a ranar Laraba, 30 ga watan Janairu.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Buhari ya umarci da a zabi Ganduje a matsayin Gwamnan Kano a zaben 2019

Dan Abia wanda ya bayar da hakuri akan kuskurensu na zuwa APC, ya kara da cewa sun yanke shawarar dawowa PDP ne bayan sun rasa martabar siyasarsu a jam’iyyar tsintsiya, inda yace APC bata da wani abun nunawa ga mutanen Akwa Ibom da ma yan Najeriya baki daya.

Shugaban PDP a yankin elder Benji Udobia, wanda yayi Magana a madadinsu ya ba Gwamna Udom Emmnuel tabbacin samun goyon bayansu wajen tabbatar da tazarcen shi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel