Rarara da Ado Gwanja sun gwangwaje a wurin kamfen din Buhari

Rarara da Ado Gwanja sun gwangwaje a wurin kamfen din Buhari

Fittatun jaruman Kannywood sun kayyatar da dandazon mutane a wurn kaddamar da yakin neman zaben Shugaba Muhammadu Buhari da aka gudanar a yau Alhamis a filin wasanni na Sani Abacha da ke Kano.

Wasu daga cikin fittatun mawakan Kannywood da su kayi waka a wurin sun hada da Ado Gwanja, Ibrahim Yala da Rarara Kahutu inda mutane suka cika da murna da annashuwa.

Masu barkwanci kamar su Baba Ari da Rabiu Daushe suma ba a bar su a baya ba inda suka fito suka rika tika rawa yayin da mawakan ke waka wanda hakan ya matukar burge mutane.

Rarara da Ado Gwanja sun gwangwaje a wurin kamfen din Buhari

Rarara da Ado Gwanja sun gwangwaje a wurin kamfen din Buhari
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Wani mai gida ya kashe matarsa saboda zargin cin amanar aure

Manyan jiga-jigan fim irin su Ali Nuhu, Sadik Sani, Zainab Booth, Rukayya Dawayya suma sun tara 'yan kalo a wani gefe guda na filin taron.

Magoya bayan jam'iyyar ta APC da suka hallarci taron kaddamar da yakin neman zaben sunyi nishadi sosai inda wasu suka rika tika rawa yayin wasu kuma suke jinjina ga mawaka da 'yan takarar na APC.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ta ruwaito cewa a farkon wannan makon wasu daga cikin jaruman na Kannywood sun gudanar da gangami domin wayar da kan magoya bayan jam'iyyar ta APC gabanin kaddamar da yakin neman zaben.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel