INEC ta amince da 'yan takarar APC na jihar Zamfara - Yari

INEC ta amince da 'yan takarar APC na jihar Zamfara - Yari

Gwamna Abdulaziz Yari na jihar Zamfara ya ce ya samu bayani cewa hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta karbi jerin sunayen 'yan takarar zabe na APC daga jihar Zamfara.

A hirar da ya yi da manema labarai a ranar Alhamis, Yari ya ce hukumar zaben ta yi biyaya da umurnin kotu da ta umurce ta karbi sunayen 'yan takarar na APC da suka lashe zabukkan fidda gwani da akayi a ranar 7 ga watan Oktoba kuma ta hana uwar jam'iyyar canja sunayen 'yan takarar da su kayi nasara.

Ya ce jam'iyyar na APC za ta shiga a fafata da ita a babban zaben da ke tafe.

INEC ta amince da 'yan takarar APC na jihar Zamfara - Yari

INEC ta amince da 'yan takarar APC na jihar Zamfara - Yari
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Kamfen din Buhari: 'Yan kasuwa a Kano sun rufe shaguna don tsoron barkewar rikici

"A yau ranar Alhamis, mun samu labarin cewa hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta karbi 'yan takarar mu kamar yadda kotu ta bayar da umurni.

"Mun sha gwagwarmaya sosai a kotu amma yanzu komi ya wuce tunda an karbi 'yan takarar mu, muna mika godiya ga shugabanin jam'iyya saboda jajircewar da su kayi saboda sun fahimci wannan wani gwaji ne mai wucewa," inji shi.

Ya ce za su tsunduma cikin yakin neman zabe a ranar Litinin da zarar Shugaba Muhammadu Buhari ya bar jihar a ziyarar da zai kawo na kadamar da yakin neman zabensa.

Ya kara da cewa akwai yiwuwar wasu da akayi karar su a kotun su daukaka kara amma ya shawarci 'yan jam'iyyar su kwantar da hankulansu domin za su bi shari'ar duk inda aka kai ta kuma yana sa ran za suyi nasara.

"Babu wani umurni da aka bawa INEC ko jam'iyya na aikata wani abu bayan hukuncin da babban kotun jiha ta yanke kuma munyi murna da hakan," inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel