Yanzu Yanzu: Buhari ya umarci da a zabi Ganduje a matsayin Gwamnan Kano a zaben 2019

Yanzu Yanzu: Buhari ya umarci da a zabi Ganduje a matsayin Gwamnan Kano a zaben 2019

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya daga hannun gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje sama a matsayin dan takarar APC

- Buhari yayi umurni da a zabe shi a matsayin gwamnan jihar karo na biyu a zabe mai zuwa

- A yau Alhamis, 31 ga watan Janairu ne dai shugaban kasar ya kaddamar da kamfen dinsa a Kano

Rahotanni da ke zuwa mana sun nuna cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya daga hannun gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje inda yayi umurni da a zabe shi a matsayin gwamnan jihar karo na biyu a zabe mai zuwa.

Shugaban kasar ya kaddamar da Ganduje a matsayin wanda jama'a kuma masoyansa za su zaba a zaben gwamna wanda za a gudanar a watan Maris.

Yanzu Yanzu: Buhari ya umarci da a zabi Ganduje a matsayin Gwamnan Kano a zaben 2019

Yanzu Yanzu: Buhari ya umarci da a zabi Ganduje a matsayin Gwamnan Kano a zaben 2019
Source: Facebook

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da mutane suka zuba idanu don ganin ko shugaban kasar zai marawa Ganduje baya sakamakon zarginsa da ake da karban na goro daga wani dan kwangila a jihar.

KU KARANTA KUMA: Yaki da Boko Haram: Shettima ya sa mafarauta 500 rantsuwa da Qur’ani da Injila

Mun kawo cewa jirgin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya tashi daga babban filin jirgin Nnamdi Azikwe Abuja zuwa filin jirgin Aminu Kano dake birnin Kano.

Mun samu wannan ne daga bakin hadimin Buhari kan sabbin kafafen yada labarai, Bashir Ahmed, inda yace: "Shugaba ya tashi daga filin jirgin saman Nnamdi Azikwe Abuja zuwa Kano, zai halarci taron yakin neman zabe a babban filin kwallon Sani Abacha."

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel