Yanzu-yanzu: CCT ta tsayar da ranar gurfanar da Onnoghen

Yanzu-yanzu: CCT ta tsayar da ranar gurfanar da Onnoghen

Kotun Da'ar Ma'aikata CCT ta tsayar da ranar 4 ga watan Fabrairu domin cigaba da sauraon shari'ar da ake yiwa Alkalin Alkalai na kasa Walter Onnoghen bisa tuhumarsa da kin bayyana wasu kadarorinsa

Wannan yana cikin wani sanarwa ce da shugaban sashin hulda da jama'a na kotun, Ibraheem Al-Hassan ya fitar a ranar Alhamis.

Yanzu-yanzu: CCT ta tsayar da ranar gurfanar da Onnoghen

Yanzu-yanzu: CCT ta tsayar da ranar gurfanar da Onnoghen
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Dakatar da Cif Joji: Matasan Kano sun ja kunnen Shugaba Buhari

Ga sakon a kasa:

"Kotun Da'ar ma'aikata ta saka ranar 4 ga watan Fabrairu domin cigaba da sauraron shari'ar da ake yiwa Hon. Jastice Walter Onnoghen a kan rashin bayyana kadarorinsa.

Bayan hukuncin da Kotun koli ta yanke a jiya a kan shari'ar CJN, Hon. Jastis Onnoghen Nkanu Walter a kan rashin bayyana kadarorinsa, Kotun Da'ar Ma'aikata ta tsayar da ranar 4 ga watan Fabrairun 2019 domin cigaba da sauraron karar.

An cimma wannan matsayar ne bayan kotun na CCT ta shigar da bukata na cigaba da shari'ar da ake yi tsakanin Gwamnatin Tarayya da Hon. Justice Onnoghen Nkanu Walter Samuel mai lamba: CCT/ABJ/01/19 da aka aike was shugaban CCT dauke da sa hannun Musa Ibrahim Usman (Esq) da Fatima Danjuma Ali (Esq)."

Dama an dakatar da sauraron shari'ar ne saboda karar da CJN, Walter Onnoghen ya shigar a kotun daukaka kara a sai dai a ranar 30 ga watan Janairu, kotun daukaka karar tayi watsi da bukatar na Onnoghen.

Wannan ne ya bawa Kotun Da'ar Ma'aikatan damar cigaba da sauraron shari'ar da ake yiwa Alkalin Alkalan da aka dakatar a halin yanzu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel