Za ai yaki idan APC ta yi magudin zabe, inji Uche Secondus

Za ai yaki idan APC ta yi magudin zabe, inji Uche Secondus

Shugaban jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na kasa Uche Secondus ya ce za ai yaki a Najeriya idan gwamnati mai ci tayi magudi a zaben shugabancin kasa da za a gudanar a watan Fabrairu.

A yayin da ya ke jawabi a garin Asaba na jihar Delta a wurin taron kaddamar da yakin neman zaben dan takarar shugabancin kasa, Secondus ya zargi gwamnatin Najeriya da tursasa Hukumar Zabe mai Zaman Kanta INEC yin magudin zabe domin su yi nasara.

Za ai yaki idan APC ta yi magudin zabe, inji Uche Secondus

Za ai yaki idan APC ta yi magudin zabe, inji Uche Secondus
Source: Depositphotos

"A yau, da izinin ku, muna yiwa INEC gargadi kuma muna kyautata zaton akwai mutanen kirki a INEC... Mun san gwamnati tana yi musu matsin lamba domin suyi magudin zabe amma idan su kayi magudin zabe, yaki suke nema," inji shi.

DUBA WANNAN: Da duminsa: Dan majalisar PDP a Ekiti ya bayyana dalilin komawa APC

Ya kuma sake tambayar mutanen da suka hallarci ko abinda ya fadi gaskiya ne kuma suka amsa cewa haka zancen ta ke.

Ya cigaba da cewa: "Idan suna son zaman lafiya, kada su sake suyi magudin zabe saboda kowa ya shirya wa wannan zaben.

"Muna son mu shawarci hukumomin tsaro, mun san akwai mutanen kirki a cikinsu da suke kare dukiyoyi da rayyukan mutane. Muna kyautata zaton za suyi biyaya ga kundin tsarin mulki, ba za su karya doka ba kamar Shugaban kasa da ke karya dokokin mu.

"Za suyi biyaya ga dokar kasa, ba za su nuna fifiko ba amma idan ba suyi hakan ba, idan suka hada baki da INEC wurin aikata magudin zabe, mene suke nema?

Mutane suka amsa da cewa, "Yaki"

Secondus ya kara da cewa: "Saboda haka muna shawartar dukkan 'yan Najeriya su fito su jefa kuri'unsu a ranar 16 ga watan Fabrairu kuma su kasa su tsare domin dole a kirka dukkan kur'iun 'yan Najeriya. Saboda mu tsige mutumin da baya iya harka da mutane, mu tsige mutumin da ya ke kunyata kasar mu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel