Yaki da Boko Haram: Shettima ya sa mafarauta 500 rantsuwa da Qur’ani da Injila

Yaki da Boko Haram: Shettima ya sa mafarauta 500 rantsuwa da Qur’ani da Injila

Domin kore shakkun da ka iya tasowa a filin daga, Gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima a ranar Laraba, 30 ga watan Janairu ya shugabanci wani rantsuwa da gwamnati ta gudanar.

Anyi rantsuwar ne ta hanyar amfani da Qur’ani da Bible sannan mafarauta da suka hada da Musulmai da Kirista 500 ne suka yi rantsuwar.

Yaki da Boko Haram: Shettima ya sa mafarauta 500 rantsuwa da Qur’ani da Injila

Yaki da Boko Haram: Shettima ya sa mafarauta 500 rantsuwa da Qur’ani da Injila
Source: Facebook

Za a dai tura wadannan mafarauta filin daga ne domin su tallafawa sojoji wajen yakar yan ta’addan Boko Haram a wasu yanunan jihar Borno.

Yaki da Boko Haram: Shettima ya sa mafarauta 500 rantsuwa da Qur’ani da Injila

Yaki da Boko Haram: Shettima ya sa mafarauta 500 rantsuwa da Qur’ani da Injila
Source: Facebook

Anyi bikin rantsuwar ne a Maiduguri inda gwamnan ya gabatar da motoxin yaki ga mafarautan sannan ya basu tabbacin cewa za a dunga biyansu alawus duk wata da kuma tallafin kayayyakin abinci ga iyalansu.

KU KARANTA KUMA: An kama wata yar shekara 35 da ta sace jariri sabon haihuwa a asibitin Anambra

Yaki da Boko Haram: Shettima ya sa mafarauta 500 rantsuwa da Qur’ani da Injila

Yaki da Boko Haram: Shettima ya sa mafarauta 500 rantsuwa da Qur’ani da Injila
Source: Facebook

A wani lamari na daban, mun ji cewa Jami’an rundunar Yansandan Najeriya sun samu nasarar kashe wani kasurgumin jagoran yan fashi da makami a jahar Enugu yayin da suka kaddamar da samame akan gungun yan fashin da yake jagoranta.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kaakakin yansandan jahar, SP Ebere Amaraizu ne ya bayyana haka a ranar Alhamis, 31 ga watan Janairu, inda yace gungun yan fashin sun saba tare hanyar 9th Mile-Udi-Oji-Awka suna yi ma matafiya fashi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel