Marafa ya yi jinjina ga INEC, yace har yanzu APC bata cire rai ba a Zamfara

Marafa ya yi jinjina ga INEC, yace har yanzu APC bata cire rai ba a Zamfara

- Sanata Kabiru Garba Marafa ya yaba ma hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) kan jajircewa da ta yi akan maganarta na farko na yin watsi da yan takarar APC a Zamfara

- Marafa ya jinjina wa Justis Ijeoma Ojukwu kan hukuncinta

- Yace APC na iya cike guraben yan takara a jihar Zamfara idan har kotun roko da ke Sokoto ta aminta da rokonsu

Shugaban kwamitin man fetur na majalisar dattawa, Sanata Kabiru Garba Marafa ya yaba ma hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) kan jajircewa da ta yi akan maganarta na farko na yin watsi da yan takarar APC a Zamfara.

An yanke hukunci biyu kan lamarin a ranar Juma’a. Wata babbar kotun tarayya karkashin jagorancin Justis Ijeom Ojukwu tace INEC ta yanke hukunci ne akan ikonta ta hanyar kin amincewa da jerin sunayen yan takara daga wani bangare na APC jihar Zamfara.

Hukunci na biyu ya fito ne daga Justis Muhammad Bello Shinkafi na wata babbar kotun Gusau, Jihar Zamfara. Shinkafi ya tabbatar da cewa an gudanar da zaben fidda gwani sannan ya ukaci INEC da ta amince da yan takarar da aka gabatar daga zaben fidda gwanin.

Marafa ya yi jinjina ga INEC, yace har yanzu APC bata cire rai ba a Zamfara

Marafa ya yi jinjina ga INEC, yace har yanzu APC bata cire rai ba a Zamfara
Source: Depositphotos

Don haka a ranar Laraba, 30 ga watan Janairu bayan nazari akan hukunce-hukuncen biyu, INEC ta yanke shawarar tsayawa akan kudirinta na farko.

Musamman hukumar a wani jawabi daga kwamishinan bayanai da wayar da kan masu zabe, Barista Festus Okoye tace, “hukumar ta yanke shawarar tsayawa akan maganarta na farko cewa jam’iyyar da ake Magana akai bata gudanar da zaben fidda gwani ba, saboda haka kamar yadda yake a sashi na 87 n dokar zaben 2010 ba ta cancanci gabatar da yan takara ba."

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Filin wasa na Sani Abacha ya zama babu masaka tsinke tun kafin isowar Buhari filin taro

Da yake martani akan haka, Marafa, babban dan takarar gwamna na APC, yace hukumar tayi abunda ya dace ta hanyar tsayawa akan maganarta game da lamarin.

Hakazalika, Marafa yayinda yake jinjina wa Justis Ijeoma Ojukwu kan hukuncinta, yace APC na iya cike guraben yan takara a jihar Zamfara, idan har kotun roko da ke jihar Sokoto ta aiwatar da rokonsu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel