Da duminsa: Dan majalisar PDP a Ekiti ya bayyana dalilin komawa APC

Da duminsa: Dan majalisar PDP a Ekiti ya bayyana dalilin komawa APC

Dan majalisar jiha mai wakiltan mazabar Emure a majalisar jihar Ekiti, Olarewaju Olayanju ya fice daga jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya koma All Progressives Congress (APC).

Ya ce jam'iyyar PDP reshen jihar Ekiti ta mutu warwas. Ya ce ba zai iya cigaba da kasancewa a jam'iyyar da babu hadin kai a tsakanin mambobinta ba.

Mr Olayanju ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar ne a wani taron manema labarai a Majalisar jihar a yau Alhamis.

Da duminsa: Dan majalisar jiha na PDP ya koma APC, ya fadi dalili

Da duminsa: Dan majalisar jiha na PDP ya koma APC, ya fadi dalili
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Wani mai gida ya kashe matarsa saboda zargin cin amanar aure

"Nayi nazari sosai a kan halin da muke ciki kuma na sanar da al'ummar mazaba ta cewa ba zan iya samar masu abinda suke bukata ba a karkashin jam'iyyar PDP.

"PDP a jihar Ekiti ta shiga rudanni a yanzu. Babu wani jagora da zai hada kan 'yan jam'iyyar wuri guda, shugabanin jam'iyyar sun rushe ta ta hanyar amfani da karfin tuwo yayin aiwatar da abinda suke so.

"Jam'iyyar ta rabe gida biyu inda wasu shugabanin jam'iyyar ke kira ga 'ya'yanta su zabi jam'iyyun adawa; jam'iyyar ta mutu warwas a jihar.

"A matsayina na mutum mai nagarta, ba zan iya zama ina yiwa jam'iyyar zagon kasa ba. Hakan yasa na koma APC," inji Mr Olayanju.

Ya ce an dade APC ba ta lashe zabe a karamar hukumar Emure ba amma daga yanzun ya yi alkawarin APC ce za ta lashe zabe a karamar hukumar.

Kakakin Majalisar jihar ta Ekiti, Adeniran Alagbada ya taya dan majalisar murnar shigowa jirgin 'Next Level'.

Ya ce duk da cewa yanzu su hudu ne 'yan APC a jihar, yana kyautata zaton wasu yan majaliar za su shigo jam'iyyar ta APC a nan gaba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel