An kama wata yar shekara 35 da ta sace jariri sabon haihuwa a asibitin Anambra

An kama wata yar shekara 35 da ta sace jariri sabon haihuwa a asibitin Anambra

Rundunar yan sandan jihar Anambra ta kama wata mata mai shekara 35, Dorathy Sunday a Izzi, jihar Ebonyi kan laifin satar jariri dan kwana biyar a duniya a wani yankin masu haihuwa na asibitin koyarwa na jami’ar Nnamdi Azikwe Nnewi, jihar Anambra.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, SP Haruna Mohammed, wanda ya sanar da batun kamun a lkacin wani taron manema labarai a hedkwatar rundunar da ke Awka, yace da misalin karfe 5:50 na yammacin ranar Laraba, 30 ga watan Janairu, jami’an yan sandan Nnewi sun kama wata Dorathy Sunday mai shekara 35 a Izzi da ke jihar Ebonyi kan satar jariri.

An kama wata yar shekara 35 da ta sace jariri sabon haihuwa a asibitin Anambra

An kama wata yar shekara 35 da ta sace jariri sabon haihuwa a asibitin Anambra
Source: Depositphotos

A cewar Mohammed, mai laifin ta saci hanya zuwa asibitin sannan ta sace jaririn dan kwanaki biyar a asibitinin inda mahaifiyar yaron mai suna Mmadu Happiness Miracle mai shekaru 22 ke kwance a Uruagu, Nnewi bayan ta je wanke kayayyakinta a harabar asibitin.

Sai dai matar bata yi nasara ba lokacin da malaman inya da ke kofar shiga asibitin suka ganta sannan suka zargi yadda take yi suka kuma ja hankalin jama’a inda aka kama.

KU KARANTA KUMA: APC ta yi babban kamu a Sokoto inda Sifawa da yan PDP 6441 suka koma jam’iyyar

A halin da ake ciki, an kwato yaron da aka sace cikin koshin lafiya sannan ana bincike akan lamarin inda daga nan za a mika mai laifin kotu don hukunci.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel