Abin kunya: Malamin addini ya dirkawa mata biyu ciki a cocinsa

Abin kunya: Malamin addini ya dirkawa mata biyu ciki a cocinsa

Wata Kotu da ke zamanta a Mapo a garin Ibadan ta raba aure tsakanin wata Grace Adekunle da Fasto Adeyemi Adekunle bisa dalilin rashin kulawa, rashin sanin ya kamata da kuma yiwa wasu mata biyu ciki da faston ya yi.

Ma'auratan sun kwashe shekaru 18 suna zaman auren kafin alkali ya raba auren a yau Alhamis 30 ga watan Janairu.

Abin kunya: malamin addini ya dirkawa mata biyu ciki a cocinsa

Abin kunya: malamin addini ya dirkawa mata biyu ciki a cocinsa
Source: Twitter

A yayin da ya ke yanke hukunci, alkalin ya ce, "Domin tabbatar da zaman lafiya da lumana, an raba auren da ke tsakanin Grace da Adeyemi.

"Adeyemi zai rike yaransu hudu na farko yayin da Grace za ta rike dan autan saboda karancin shekarunsa.

"Wanda akayi karar zai rika biyan N5,000 duk wata domin kula da yaron baya ga biyan kudin makarantarsa da wasu kulawa."

DUBA WANNAN: Wani mai gida ya kashe matarsa saboda zargin cin amanar aure

A karar da ta shigar, matar wadda malamar makaranta ce ta sanar da kotu cewa mijinta wanda fasto ne ya yi watsi da ita sannan ya fara kwanciya da matan cocinsa.

"Da farko Adeyemi baya kulawa da ni da kuma yaran mu biyar tun bayan da ya zama fasto wasu shekaru da suka wuce.

"Baya ciyar da su balle biyan kudin makarantarsu.

"Ya sha nanata min cewa ba zai iya biyan kudin makarantar yaran mu ba saboda shi fasto ne kuma talaka, ya ce na san cewa shi fasto ne kafin in aure shi.

"Sakamakon hakan dukkan yaran mu masu shekaru 8 zuwa 16 ba su zuwa makaranta a halin yanzu.

"Na kashe dukkan kudin da na ke dashi a kansu amma babu wani takamamen nasara.

"Abin haushi kuma shine Adeyemi yana neman matan da ke cocinsa har ma ya yiwa guda biyu daga cikinsu ciki," inji Grace.

Sai dai mijin bai hallarci kotun ba balle ya kare kansa daga zargin da ake masa duk da cewa an aike masa da sammaci sau da yawa inji jam'in kame na kotun.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel