Sabbin kusoshi da Obasanjo ya aikowa Buhari a yau

Sabbin kusoshi da Obasanjo ya aikowa Buhari a yau

- Obj baya so Buhari ya zarce

- Tagomashinsa ya ragu sosai har Tinubu ya ishi a yankinsu

- Amma kuma yana da manyan abokai masu iko

Sabbin kusoshi da Obasanjo ya aikowa Buhari a yau

Sabbin kusoshi da Obasanjo ya aikowa Buhari a yau
Source: Facebook

A wannan karon, dattijo Obasanjo, ya sake caccakar Buhari ne kan salon mulki, inda ya kira shi da wanda bai san ta kan tattalin arziki ba, kuma bbai iya sama wa jama'a aikin yi ba sai rabon kudi, makonni biyu kafin zabe.

Obasanjo, ya kuma ce ko a tsaron ma da ya dauka Buhari zayyi wani katabus, bayyi ba, kuma ya kara ce masa wanda yake zabar ko suwaye zai yi wa zargin cin hanci, banda mukarrabansa.

GA WANNAN: Cin hanci ya karu a Amurka, bayan da ya sauka a Najeriya, a sabon rahoton masu sanya idanu

Tun cikin 2016 dai aka sami manya-manyan laifuka na cin hanci da ake zargin abokan Buharin da aikatawa, amma sai a yanzu a wannan makon ne aka shigar da kararsu, ganin kowa na cewa ai ya kamata ace tuntuni sun shiga kurkuku kamar saura.

A yau ma dai an shigar da karar Babachir Lawal, wanda yake SGF da aka dade ana zarga da cin hanci, sai dai kuma an gano Buharin yana daga hannun Ganduje, wanda shima dumu-dumu aka ga bidiyonsa yana amsar daloli da ya kamata ace a banki aka yi hada-hadarsu in dai da gaskiya.

Saura makonni biyu a zabi Atiku a matsayin shugabann Najeriya, ko a zartas da Buhari.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel