Martanin gwamnati kan wai ko sabon CJN baije makarantar sharia ba

Martanin gwamnati kan wai ko sabon CJN baije makarantar sharia ba

- An karyata zargin da akeyi na cewa alkalin alkalai baije makarantar lauyoyi ba

- An rantsar dashi a matsayin lauya a shekarar 1981

- Zargin da ake masa mara tushe ne

Martanin gwamnati kan wai ko sabon CJN baije makarantar sharia ba

Martanin gwamnati kan wai ko sabon CJN baije makarantar sharia ba
Source: UGC

An karyata zargin da rade radin da akeyi na cewa alkalai na Justice Tanko Muhammad ba cikakken lauya bane kuma baije makarantar lauyoyi ta Nigeria ba wato Nigerian law school balle a rantsar dashi a matsayin cikakken lauya.

Bincike dai ya tabbatar da cewa wannan batu zargi ne da bashi da tushe balle makama domin kuwa justice Tanko Muhammad cikakken lauya ne Wanda yayi karatun aikin lauyanci a jami'ar Ahmadu bello dake Zaria daga shekarar 1976 zuwa 1980 kuma yaje makarantar lauyoyi a shekarar 1981 inda aka rantsar dashi.

DUBA WANNAN: OhanaEze Buhari zasu yi

Sashe na 231 na kundin tsarin mulkin Nigeria ya tanadi cewa tilas sai an mutun yayi makarantar lauyoyi sannan yake da damar yin aikin lauyanci kuma justice Tanko Muhammad duk yayi wadannan karatuttukan.

An dai nada justice Tanko Muhammad a matsayin mukaddashin alkalin alkalai bayan dakatar da tsohon alkalin alkalan Onnogen da shugaba Muhammadu Buhari yayi. Hakan ya janyo kace nace a tsakanin yan kasa musamman kunguyoyin lauyoyi da suke goyon bayan tsohon alkalin.

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng Read more: https://hausa.legit.ng/1218525-fin-rabin-biliyan-pencom-ta-kwato-wa-masu-fansho-daga-guminsu-na-karshen-2018.html

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel