'Daga Buharin har Atiku bana yi' inji Wole Soyinka

'Daga Buharin har Atiku bana yi' inji Wole Soyinka

- Sanannen marubuci Wole Soyinka yace baya goyon bayan Buhari ko Atiku

- Marubucin yace lokaci yayi da kasar nan zata canza akala

- Nan ba da dadewa ba kungiyoyin su zasu sanar da Dan takarar da ya dace a zaba

'Daga Buharin har Atiku bana yi'

'Daga Buharin har Atiku bana yi'
Source: Depositphotos

Wole Soyinka, kwararre kuma sanannen marubuci yace ba zai goyi bayan yan takara biyun ba na fitattun jam'iyyun siyasar da suka fito takarar shugabancin kasa.

Yace hakan ne a zauren tattaunawa na yan kasa a na 2019.

"Lokaci ne yanzu na sabuwar alkibla kuma idan wani dan takara ya bayyana zamu bashi goyon baya," a cewar shi.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP sune yan takara biyu dake kan gaba.

Dan shekaru tamanin din yace yanzu lokaci ne na canza alkiblar kasar nan ta hanyar da ya dace.

"Don gujewa tantama, bari in fadi matsayata saboda bana son in zama mai harshen damo; Ni Wole Soyinka bazan zabi kowa dag cikin sanannun yan takarar biyu ba. Na gaba cewa dukkanin su basu cancanci kuri'a ta ba," inji shi.

GA WANNAN: Cin hanci ya karu a Amurka, bayan da ya sauka a Najeriya, a sabon rahoton masu sanya idanu

"A saboda dalilai na wadanda ba sai na bayyana ba, banda ra'ayin su. Matsayata mai sauki ce, itace lokaci yayi da zamu canza alkibla. Kuma kiri kiri ba ni kadai bane, akwai wata kungiya dake taro a Legas don fitar da Dan takara daya da ta yarda dashi. Akwai wata kungiyar a Abuja ma wacce daga karshe zasu sanar damu dan takarar da ya dace. Ana abubuwan sirri don ganin an canza akalar kasar nan ta hanyar da ta dace, kuma a ganar da mutane cewa bai kamata su bautar da kansu har abada ba ga tsofaffin dokoki."

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel