Yadda na hana wani tshohon gwamna dawowa kujerarsa – Atiku

Yadda na hana wani tshohon gwamna dawowa kujerarsa – Atiku

- Dan takarar Shugaban kasa, Atiku Abubakar yace yana da hannu wajen hana Chinwoke Mbadinuju zarcewa a matsayin gwamnan jihar Anmbra a 2003

-Atiku wanda ya kasance mataimakin Shugaban kasa a waccan lokacin yace Mbadinuju bai yiwa fannin ilimi na jihar kokari ba ko kadan

- Mbadinuju ya lashen zaben fidda gwani na gwamnan PDP a 2003 amma aka ambaci Chris Ngige a matsayin dan takarar jam’iyyar

Dan takarar kujerar Shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) kuma tsohon mataimakin Shugaban kasa, Atiku Abubakar yace yana da hannu wajen hana Chinwoke Mbadinuju zarcewa a matsayin gwamnan jihar Anmbra a 2003.

Yayinda yake amsa tambayoyi a wani shirin talbijin kan zaben 2019, Atiku wanda ya kasance mataimakin Shugaban kasa a waccan lokacin yace Mbadinuju bai yiwa fannin ilimi na jihar kokari ba ko kadan wanda acewar Atiku shine mafi daraja a wajensa.

Yace shi ya shawo kan Obasanjo cewa su yi adawa da Mbadinuji.

Yadda na hana wani tshohon gwamna dawowa kujerarsa – Atiku

Yadda na hana wani tshohon gwamna dawowa kujerarsa – Atiku
Source: UGC

“A lokacin da nake mataimakin Shugaban kasa na je wani rangaji Anambra a lokacin gwamnatin Chinwoke Mbadinuju, sai na gano ciyayi sun kewaye dukkanin makarantun gwamnati.

KU KARANTA KUMA: APC ta yi babban kamu a Sokoto inda Sifawa da yan PDP 6441 suka koma jam’iyyar

“Sai na koma ga Shugaban kasa sannan nace ya zama dole kada a bari wannan gwamnan ya dawo, kuma ku yarda dani bai dawo ba," inji Atiku.

Mbadinuju ya lashen zaben fidda gwani na gwamnan PDP a 2003 amma aka ambaci Chris Ngige a matsayin dan takarar jam’iyyar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel