Zaben 2019: 'Yan kasuwan canji sun koka kan rashin samun ciniki

Zaben 2019: 'Yan kasuwan canji sun koka kan rashin samun ciniki

- Masu sana'ar canjin kudi a garin Benin sun koka a kan rashin kasuwa a yayin da zabe ke karatowa

- Masu canjin sun ce sunyi tsamanin kasuwa za ta bude sosai saboda zabe ya matso amma sun ka akasin hakan

- 'Yan canjin sun danganta rashin samun cinikin da yaki da rashawar da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ke yi

Masu sana'ar canjin kudi a garin Benin sun koka kan rashin samun ciniki duk da cewar ana fuskatar babban zabe na kasa da za a yi a watan Fabrairu.

Wasu daga cikin 'yan canjin sun shaidawa Kamfanin Dillanci Labarai na kasa NAN a hirar da akayi da su lokuta daban-daban a ranar Alhamis 30 ga watan Janairu cewar ba su samun ciniki a maimakon yadda suka samu a zaben da ta gabata.

Zabe: 'Yan canji sun koka kan rashin samun ciniki a yanzu da zabe ke karatowa

Zabe: 'Yan canji sun koka kan rashin samun ciniki a yanzu da zabe ke karatowa
Source: Getty Images

DUBA WANNAN: Dakatar da Onnoghen: Matasa sun yiwa shugaban kungiyar lauyoyi duka a jihar Ribas

'Yan canjin sun ce sunyi tsamanin za su samu kasuwa sosai dubba da cewa babban zabe na kasa ya matso amma har yanzu ba bu wani cinikin azo a gani.

Sun ce a lokacin irin wannan, yan siyasa su kan riga yin rige-rige zuwa wurinsu domin canja Dalolinsu zuwa Naira.

Shugaban kungiyar United Bureau De Change Traders Association a Erie da ke Benin, Jamilu Suleiman ya ce ya yi imanin cewa yaki da rashawa da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari keyi na daga cikin dalilin da yasa ba su samun ciniki kamar yadda ya ke a baya lokutan zabe.

Ya ce: "Haka bai taba faruwa da mu a lokacin zabe ba; a gaskiya bamu samun ciniki sosai abinda dai sai a hankali.

"A shekarun baya irin wannan lokacin a kan samu riba sosai saboda zabe. A yanzu din ma muna gudanar da kasuwancin mu kamar yadda muka saba amma bamu samu irin kasuwar da muke tsamani a lokacin zabe ba.

"Ina kyautata zaton wannan rashin cinikin ba zai rasa nasaba da yaki da rashawa da Shugaba Muhammadu Buhari ke yi ba, 'yan siyasa na tsoron kada a kama su."

Wani mai sana'ar canjin, Haruna Adamu shima ya ce ba su caba ciniki kamar yadda su keyi a lokutan zabe a shekarun baya.

Ya ce: "Idan da a shekarun baya ne, da ba zan sami lokacin wanna hirar da ku ba saboda mutane za su cika shago na makil.

"Ba mu farin ciki da hakan, ina fatan abubuwa za su canja kafin a fara zaben."

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel