Yakin Zabe: Buhari ya ziyarci jihar Kano

Yakin Zabe: Buhari ya ziyarci jihar Kano

A yanzu din nan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dira a jihar Kano a yayin da ya ke ci gaba da shawagi da yawon karade jihohin 36 da ke fadin kasar nan domin gudanar da yakin sa ne neman zaben da girgiza magoya baya.

Yakin Zabe: Buhari ya ziyarci jihar Kano

Yakin Zabe: Buhari ya ziyarci jihar Kano
Source: Twitter

Jirgin da ya yo jigilar shugaban kasa Buhari ya sauka a filin jirgan saman Barikin sojin sama da ke cikin garin Kano da misalin karfe 1.00 na ranar Yau Laraba kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito.

Bayan kai ziyarar ban girma zuwa fadar mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi na biyu, shugaban kasa Buhari zai kuma gudanar da taron yakin neman zaben sa a harabar filin wasanni na Sani Abacha da tuni ya dinke da al'umma.

KARANTA KUMA: Buhari ya tafka kuskure wajen mu'amalantar masu akidar Shi'a - Atiku

Babban hadimi na musamman ga gwamnan Kano Abudallahi Ganduje akan sabuwar hanyar sadarwa ta zamani, Salihu Tanko Yakasai, shine ya bayar da shaidar wannan rahoto a shafin sa na zauren sada zumunta.

Tawagar da ta tarbi shugaban kasa Buhari ta hadar da gwamnan Kano tare da mataikin sa, Yusuf Gawuna, Ministan harkokin cikin gida, Abdulrahman Dambazau, tsohon Mataimakin gwamnan jihar Kano, Farfesa Hafiz Abubakar da kuma gwamnonin jihar Zindar da Maradi na kasar Nijar.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel