An gudanar da gangamin goyon bayan shugaba Buhari a birnin New York na Amurka (Hotuna)

An gudanar da gangamin goyon bayan shugaba Buhari a birnin New York na Amurka (Hotuna)

Jama’a da dama da suka kunshi yan Najeriya mazauna kasashen waje da turawa sun gudanar da gangamin zanga zanga a gaban ofishin jakadancin Najeriya dake birnin New York na kasar Amurka, inda suka yi kira ga kasar Amurka ta mara ma Buhari baya.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito masu zanga zangar sun shiryata ne domin bayyana ma duniya goyon bayansu ga shugaban Nejeriya Muhammadu Buhari tare da bashi kwarin gwiwa bisa kokarin da yake yi na yaki da rashawa a kasar.

KU KARANTA: Zan dauki tsatstsauran matakai akan kwamandojin rundunar Sojin Najeriya –Atiku

An gudanar da gangamin goyon bayan shugaba Buhari a birnin New York na Amurka (Hotuna)

Zanga Zangar
Source: UGC

Musamman sun hada gangamin ne domin nuna ma duniya cewa basa tare da korarren tsohon alkalin alkalai, Walter Onnoghen wanda ake zargi da boye siye da naira biliyan 1 asusun bakinsa, haka zalika suna goyon bayan matakin tsigeshi da Buharin yayi.

Bugu da kari, yan zanga zangar sun yi kira ga gwamnatin kasar Amurka, da majalisar dinkin duniya dasu mara ma Buhari baya game da yakin da yake yi da mazabta, mahadanma da yan wawura masu burin karya Najeriya domin biyan bukatunsu.

An gudanar da gangamin goyon bayan shugaba Buhari a birnin New York na Amurka (Hotuna)

Zanga Zangar
Source: UGC

Idan za’a tuna shugaba Buhari ya sallami Onnoghen ne bayan bayyanar wasu bayanai masu karfi dake nuni da cewa ya boye wasu makudan kudade a asusun bankinsa ba tare daya bayyanasu kamar yadda doka ta tanada ba.

Kudaden wadanda idan aka juyasu zuwa kudin Najeriya sun haura naira biliyan daya, ya boyesu ne cikin asusun banki daban daban a dala, fam da yuro, haka zalika ya mallaka sama da gidajen hamsin, wadanda duka ya boye ma hukuma.

An gudanar da gangamin goyon bayan shugaba Buhari a birnin New York na Amurka (Hotuna)

Zanga Zangar
Source: UGC

Sai dai Onnghen bai amince da sallamar da aka yi masa ba, inda ya garzaya gaban kotun daukaka kara domin samun kariya daga tuhumar da ake masa a gaban kotun da’ar ma’aikata, CCB, amma a can ma bai sha ba, inda kotun ta umarceshi daya koma CCB domin amsa tuhume tuhumen dake wuyansa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel