Lalata fostocin zabe a Kano: APC da PDP sunyi musayar kalamai masu zafi

Lalata fostocin zabe a Kano: APC da PDP sunyi musayar kalamai masu zafi

Jam'iyyun siyasa na All Progressive Congress (APC) da Peoples Democratic Party (PDP) suna musayan maganganu a kan zargin lalata fostoci da allunan yakin neman zabe da akayi a jihar Kano.

Jam'iyyun biyu suna zargin juna da saba alkawurran da su ka rattaba hannu a kai a cikin yarjejeniyar zaman lafiya da wakilan su suka amince da ita.

Alhaji Sanusi Bature Dawakin Tofa, hadimin dan takarar gwamna na jam'iyyar PDP a jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusif ya zargi jam'iyyar APC da lalata fostocin PDP a cikin wata sako da ya fitar.

Lalata fostocin zabe a Kano: APC da PDP sunyi musayar kalamai masu zafi

Lalata fostocin zabe a Kano: APC da PDP sunyi musayar kalamai masu zafi
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Dakatar da Onnoghen: Matasa sun yiwa shugaban kungiyar lauyoyi duka a jihar Ribas

"Ran mu ya baci kan yadda ake lalata fostoci da allunan yakin neman zaben jam'iyyar PDP a jihar Kano.

"Mun samu rahotannin cewa wasu 'yan bangan siyasa da muke kyautata zaton APC ta dauki nauyi suna kai hari ga magoya bayanmu a cikin gari gabanin zuwar Shugaba Muhammadu Buhari a yau," inji shi.

Dawakin Tofa ya yi kira ga magoya bayan jam'iyyar PDP na Kwankwasiyya su kwantar da hankalinsu kuma su guji zuwa wuraren da 'yan APC za su ziyarta a yau.

A bangarensa, Kwamishinan yada labarai na Kano, Malam Muhammadu Garba ya musanta zargin inda ya ce 'yan Kwankwasiyyar sun bijiro da wanna karyar ne domin su kawar da hankulan mutane a kan hare-haren da suka kai a kan al'umma yayin rally da su kayi a Kano Municipal da karamar hukumar Tarauni.

Garba ya ce 'yan Kwankwasiya sun kidime ne saboda rahotannin da aka wallafa a rediyo da jaridu da ke nuna mambobinsu dauke da makamai inda suke lalata motocci, babura da kai wa mutane hari.

"Ba zamu amince da wannan karerayin da suke yadawa ba domin kawar da hankulan mutane a kan barnar da suka aikata.

"Su sani cewa muna da masaniya a kan tuggan da suke kulawa na razana al'ummar jihar Kano domin batawa jihar da jam'iyyar APC suna.

"Abin kunya ne yadda 'yan kungiyar suke tayar da fitina a jihar. Ba su son zaman lafiyar da gwamnatin jihar Kano na yanzu ta samar a jihar saboda bamu musguwana abokan hammaya. Ayyuka muke tallatawa a kamfen din mu," inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel