Buhari ya tafka kuskure wajen mu'amalantar masu akidar Shi'a - Atiku

Buhari ya tafka kuskure wajen mu'amalantar masu akidar Shi'a - Atiku

- A karo na farko Atiku ya tsoma bakin sa kan dambarwa ta rikicin masu akidar Shi'a da kuma rundunar sojin Najeriya

- Atiku ya ce ba bu dace cikin kisan kiyashi da rundunar sojin ta yiwa masu akidar Shi'a yayin zangar-zangar da suka gudanar shekaru uku da suka gabata

- Makusanta sun ce Atiku ya guji tsoma baki akan rikicin domin gujewa haddasa rabuwar kai a tsakanin al'umma yayin da zaben kasa ya gabato

A jiya Laraba 30 ga watan Janairu, dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bayyana ra'ayin sa dangane da yadda gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi riko da masu akidar Shi'a.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi kaca-kaca tare da Allah wadai dangane da yadda rundunar dakarun sojin kasa ta Najeriya ta yiwa magoya baya da masu akidar Shi'a kisan kiyashi tsawon shekaru uku da suka gabata.

Buhari ya tafka kuskure wajen mu'amalantar masu akidar Shi'a - Atiku

Buhari ya tafka kuskure wajen mu'amalantar masu akidar Shi'a - Atiku
Source: Twitter

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa, kungiyar masu akidar Shi'a ta Najeriya wato IMN, Islamic Movement of Nigeria, ta yi asarar daruruwan rayukan mambobin ta a hannun rundunar sojin kasa ta Najeriya yayin bakin gumurzu da wakana tsakanin su cikin garin Zaria tun a shekarar 2015 da ta gabata.

A karo na farko, Wazirin Adamawa ya bayyana ra'ayin sa kan dambarwar masu akidar da gwamnatin Najeriya yayin zaman sauraron ra'ayin al'umma wanda gidan talabijin na kasa ya daukin nauyin gudanarwa a daren jiya na Laraba.

Atiku ya kausasa harshe tare da bayyana damuwa musamman dangane da yadda rundunar sojin kasa ta salwantar da kimanin rayukan masu akidar shi'a arba'in yayin zanga-zangar da suka gudanar cikin birnin Abuja tsakanin ranakun 27 zuwa 29 na watan Oktoba a shekarar 2015.

KARANTA KUMA: Ba ni da ikon yaye talauci a jihar Adamawa - Atiku

Turakin Adamawa ya kara da cewa, rundunar sojin kasa ta Najeriya tayi kuskure na mu'amalantar masu akidar Shi'a da a cewar sa lamari ne da ya shafi hukumar tsaro ta 'yan sanda mai nauyin kwantar da duk wata tarzoma a tsakanin al'umma.

Rahotanni kamar yadda makusantan sa suka ruwaito, Atiku ya kauracewa tsoma baki cikin dambarwar da ta gudana tsakanin rundunar sojin Najeriya da masu akidar Shi'a domin gujewa kawo rabuwar kai ta fuskar addini a yayin da babban zaben kasa ya gabato.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel