Buhari, Atiku da sauransu za su sake shiga wata yarjejeniya

Buhari, Atiku da sauransu za su sake shiga wata yarjejeniya

- Shugaban kungiyar zaman lafiya na kasa Janar Abdulsalami Abubakar, yace dukkanin yan takarar Shugaban kasa za su sake shiga wata yarjejeniyar zaman lafiya

- Abdulsalami yace yan takarar za su sanya hannu a yarjejeniyr domin amincewa da sakamakon zabe idan aka yi cikin gaskiya da amana

- A ranar 16 ga watan Fabrairu ne dai za a gudanar da zaben shugaban kasa

Shugaban kungiyar zaman lafiya na kasa kuma tsohon Shugaban kasa a mulkin soja, Janar Abdulsalami Abubakar, yace dukkanin yan takarar Shugaban kasa za su sake shiga wata yarjejeniyar zaman lafiya a wata mai zuwa.

Da yake Magana a wani taro kan zaman lafiyar zabe a Kaduna a jiya, Laraba, 30 ga watan Janairu, Abdulsalami yace yan takarar za su sanya hannu a yarjejeniyr domin amincewa da sakamakon zabe idan aka yi cikin gaskiya da amana.

Buhari, Atiku da sauransu za su sake shiga wata yarjejeniya

Buhari, Atiku da sauransu za su sake shiga wata yarjejeniya
Source: UGC

Abdulsalami wanda ya samu wakilcin daraktan kungiyar zaman lafiyan na kasa Rev. Father Atta Barkindo, yace shiga sabuwar yarjejeniyar zaman lafiyan zai kasance ne saboda dakile rikicin zabe kamar yadda yake gudana yanzu haka a kasar Sudan da sauran kasashen Afrika.

A halin da ake ciki, Atiku Abubakar, dan takarar Shugaban kasa a jam’iyar Peoples Democratic Party (PDP), yace zai yarda da kaye idan har ya fadi zaben 2019, wanda aka gudanar akan tafarkin gaskiya a amana.

KU KARANTA KUMA: Kungiyar Arewa ta marawa Buhari baya akan dakatar da Shugaban alkalan Najeriya

Mista Abubakar yace ya amince da kaye a lokacin da ya fadi a baya sannan bai ga dalilin da zai sa wannan zai zamo mai wahala ba.

Mista Abubakar ya fito ne a wani shirin gidan talbijin na yan takara da yar jarida Kadaria Ahmed ta gudanar a NTA a daren ranar Laraba, 30 ga watan Janairu. Mataimakin Atiku, Peter Obi ma ya halarci taron.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel